Tarihin Makadan Hausa Tare Da Awwal Mu’azu

Alhaji Sa’idu Mai Daji Sabon-Birni:

Haihuwarsa

An haifi Alhaji Sa’idu Mai daji a garin Tara ta sarkin kwanni, ita kuma Tara tana bin Sabon-Birni ta sarkin Gobir, jihar Sakkwato. Sannan mahaifinsa shi ne Mainasara. Ya kiyasta cewa yana da shekara arba’in da biyar (45), watau ke nan an haife shi a wajejen 1938.

Dalilin kiransa Maidaji shi ne, a lokacin rayuwar mahaifinsa suna zaune ne a tsohon garin Tara. Sai wata rigima da fadace-fadace ta haddasu tsakanin mutanen Tarar, sai aka yi ta tashi ana barin garin, bayan kuwa har sun yi shuka. Mahaifinsa Mainasara, ya ce shi kam ba zai bar shukarsa ta lalace a banza ba, sai dai a koma gona. A gonar ya gyara wurin zama, suka zauna tare da sauran ‘yan’uwansa. Watau inn wannan zama shi ne ake cewa zaman gona. Ba sa zuwa gari wata kila sai ran kasuwa ko Juma’a. To, bayan da aka koma ne gidan gona aka haifi Maidaji, da ma an tafi da cikinsa yana tsoho. Daga nan, sai mahaifinsa ya ce: “An sami Maidaji”, watau dan gidan gona.

Suna nan zaune har Maidaji ya girma, sai ruwa ya malale wurin, ya rusa wasu ‘yan gine-ginen da suka yi, sai mahaifinsa da shi da sauran iyalinsa suka bar gidan gona na Tara, suka koma Rambadawa. Rambadawa tana bin Sarkin Kwannin Tara ne, Tara kuma tana bin Sarkin Gobir na Sabon-Birni

Kuruciyarsa

Ba sai an ce maidaji ya yi noma ba, domin da jin yadda aka haife shi, da inda yake zaune bayan haihuwarsa, an san ya tashi cikin noma ne. Tun yana karami ya ke noma, har ya shahara gare shi.

Bayan noma, ya taba karatun allo. Ya yi tafiye-tafiye don yawon makaranta. Ya je kamar Mai Lalle da Tsamaye. Yawanci Mai daji da abokansa sukan sauka a wajen wani Sarki ne ko Hakimi da suka tabbata yana da abinci. Za su yi yarjejeniya da Sarkin cewa ya dinga ciyar da su, su kuwa su rika yi masa noma idan sun dawo daga aikin gona, sai su yi karatunsu na allo da ya kawo su. don haka, duk inda suka tafi ba sa yawon bara, kuma ya yi karatun yaki da jahilci tun farkon kafa shi a kauyensu, amma bai dade a ciki ba.

Waka da kida

Alhaji Sa’idu Mai daji; ya yi gadon kida da waka ne. Domin mahaifinsa ya yi, kuma wansa Nadada shi yake yi. Hasali ma, shi ne makada na garin. Sannan wani wansa kuma wanda ake kira Alhaji Mai gari yana yin kidan har yanzu.

Maidaji, ko dayake ya tashi cikin waka bai koye ta a wajen mahaifinsa ba. Wansa Nadada hi ne ya yi tashen waka kwarai. Ya yi wakoki da dama, sannan yana da basira da hikima a wajen shirya wakokinsa.

Bayan haka, ya yi makarantar allo har ya sauke. Kuma shi ma yayi karatun yaki da jahilci. Daga cikin ire-iren wakokinsa akwai:

Kidan Noma

Kidan Fada

Ya yi tafiye-tafiye da dama zuwa garuruwa don waka. Daga cikin yaransa da ke amsa masa waka, akwai:

(i) Alhaji Maigari — kanensa ne

(ii) Na Gambo Roko —kanen tsohonsa ne

(iii) Marafa—kanensa ne

(ib) Sa’iduMai daji—kanensa ne, mai kidan kanzagi

Fara wakarsa

Mai daji Sabon-Birni ya fara waka tun yana dan karami. Yana bin yara Yan’uwansa gona, idan suna noma, shi ko ya dinga yi musu ‘yan wake-wake. Daga nan ya fara zuwa da wasu yara suna amshi, wasu kuma suna kida da gwangwani; sai kuma aka fara gayyatarsa ya je kida na gayya.

Ya koyi kida da waka na sosai a wajen wansa Nadada. Kuma ya fara da kidan kurkutu ne, sai kuma ya shiga cikin masu amshi, kamar dai yadda ya gabata. Ko da yake Mai daji yana tare da wansa wajen kida, amma yakan yi gayauna ya tafi ya dinga yi wa wasu mutane ‘yan wake-wake a gona ko a kasuwa da sauran wurare.

Wakar noma ta farko wadda ya yi, ita ce wakar da ya yi wa Sarkin noma Arzika. Ita Ce:

Gindi: Sarkin yai abin daka ya huta,

Zaki dan Abubakar dan Buda.

Arzika jikan Salau Magajin Sanda,

Bai ci amanar gida ba, balle daji.

Arzika dan Imamu bawan Allah,

Bai ci amanar gida ba balle daji:

Bayan wannan waka ya ci gaba da yin wakokin noma.

Kafin makada Nadada ya bar waka, sai da Mai daji ya san wani abu dangane da dabara da hikimar shirya waka. Ya kai fagen ya yi jagorancin waka. Bayan rasuwar Makada Nadada sai Sa’idu Maidaji ya haye khalifarsa. Ya ci gaba da shugabancin waka. Yanzu ma shi né makadan garin Rambadawa, ko da yake sarkin Gobir na Sabon-Birni yana son ya koma wajensa

Ire-iren wakokinsa

Bayan da Maidaji ya hau gadon shugabancin waka sai ya dinga yin wakokin fada, gami da maimaita wadanda wansa Nadada ya yi. Sai ya kasance yana irin wadannan kade-kaden ne:

(i) Kidan noma (manoma)

(ii) Kidan Fada (Sarakuna)

(iii) Kidan Siyasa

(ib) Kidan Jama’a (talakawa).

Tsara wakarsa

Maidaji yakan sami bayanan da zai shirya waka da su ta wadannan hanyoyi:

Samun bayanai daga wajen wadanda zai shirya wa waka su kansu.

Samun bayanin Sarki ko hakimi daga bakin talakan garin ko Bafadensa Yakan tambayi nasabar Sarkin, iyayensa da kakanninsa.

Marokansa, watau yána aiken marótinsa ya tambàyo bayaflifl mutümin. Ko kumá bayanin wanda ya yi masa kyauta a lokacin da yake yin waka.

Maidaji kuma yakan yi wa wani waka saboda:

irin bajinta da kokari ko himma da manomi ya nuna. Wadannan halaye sukan sa ya yi wa mutum wada ko bai neme shi da yin haka ba.

Ko kuma idan shi kira shi da ya yi wakar.

Yakan tsara wakokinsa ta wadannan hanyoyi.

Ya tsaya gida ya shirya wada a natse.

Wannan kuwa yakan tsara ta inda duk ta samu.

Yaransa ‘Yan amshi/mataimaka

Mafi yawan yaransa daga kannensa, sai kanen tsohonsa, sai wansa, sai kuma ‘ya’yansa, kamar yadda aka bayyana a baya, dama gidansu gidan waka ne. Ga sunayen yaran:

(i) Tanko Ibrahim kanen mahaifinsa ne.

(ii) Alhaji Mai Gari—wansa ne

(iii) Hana —dansa ne

(ib) Baciri — dansa ne

(b) Abara — dansa ne

(bi) Sallau – dansa ne

(bii) Garba na mai kosai dansa ne

(biii) Dogo — dansa ne

(id) Dan Malam — dansa ne

(d) Ibrahim — marokinsa kuma baransa ne.

 

Wadanda yake yi wa wakokin noma

 

Mai daji yana yi wa kowane manomi waka, musamma ma wanda ya nuna kwazo da bajinta da kuma wanda ya masa wata gagarumar kyauta ta kasaita.

Shahararsa

Maidaji Sabon-Birni ya shahara sosai dangane da waka musamman ma wakokin noma. Wakokin Mai daji na Sabon-Birni. sun kai wurare da yawa. Akan sa su gidajen Rediyo, musamman Rediyon Rima, Sakkwato da na Tarayyar Nijeriya a Kaduna. Sannan kuma akan sa su Gidajen Rediyo masu hoto, da sauran wurare.

Malamai da dalibai daga Jami’o’i daban-daban sukan same shi har gida don bincike a kan wakokinsa. Mai daji ya yi wakoki da dama fiye da wakoki (1,000), na wakokin noma da wakokin sarauta da na sauran talakawa.

Maidaji yana da mata uku da kuma ‘ya’ya shida duk kuma rayayyu, a garin Rambadawa kilomita ishirin da biyu (22) daga sabon-Birni kuma tafiya ce ta rairayi da burji, ba kwalta ba.

 

Exit mobile version