ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

 2027: Ƙaruwar Ta’addancin Siyasa Na Haifar Da Fargabar Yaƙin Neman Zaɓe A Jihohi

by Yusuf Shuaibu
3 weeks ago
Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Rahotanni sun nuna cewa tun bayan fara yakin neman zabe a ranar 19 ga Agusta, an samu kai harehare da dama da aka danganta da ‘yan siyasa masu tayar da tarzoma a Kogi, Benuwai, Kano, Inugu, Kaduna, Delta, Ribas da wasu jihohi. 

A wasu daga cikin abubuwan da suka faru, shugabannin jam’iyyun siyasa da magoya bayansu sun ji rauni, wanda ya haifar da damuwa game da tsaron ‘yan siyasa kuma ya sa fargaba a zukatan al’umma, musamman wadanda suke son goyon bayan ‘yan takararsu a fili yayin da zaben ke karatowa. 

A yayin da jam’iyyar da ke mulki ta APC ta yi zargin aka kai wa mambobinta da magoya bayanta farmaki, yawancin rahotannin abubuwan da suka faru sun fi mayar da hankali kan mambobi da magoya bayan jam’iyyun adawa. 

ADVERTISEMENT

Yawancin hare-haren da ake zargin an kai su ne kan mambobin jam’iyyar NDC da jam’iyyar ADC da jam’iyyar PDP. 

Jihar Kogi 

LABARAI MASU NASABA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

A ranar 15 ga Satumba, wasu ‘yan ta’addan siyasa da ake zargin ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki sun hana taron da ADC ta shirya a Ejule, karamar hukumar Ofu ta Jihar Kogi, inda suka tilasta wa mambobin jam’iyya da magoya bayansu gudu don neman tsira. 

A cewar rahotanni, abin ya faru ne a lokacin da ake zargin masu kai hari sun harba bindigogi a sama, wanda ya haifar da firgici a tsakanin mahalarta taron da mazauna yankin. 

Akalla daya daga cikin mambobin ADC ya ji rauni a lokacin harin kuma aka kai shi asibiti don samun kulawar likita.Mummunan lamari ya tada sabbin damuwa kan halin tsaro a karamar hukumar Ofu, saboda akwai tarihin tashin hankali da ake yi na siyasa a yankin, musamman a lokacin zabe. 

Idan za a iya tunata a shekarar 2019, shugabar mata ta jam’iyyar PDP a Jihar Kogi, Salome Abuh an ruwaito cewa an kona ta har lahira a gidanta a wannan karamar hukuma a yayin zaben gwamna. 

Jihar Benuwai

A ranar 8 ga Satumba, an kai hari ga motar yakin neman zaben shugaban kasa na NDC, Peter Obi, wanda ake zargin cewa wasu ‘yan daba sun toshe hanya a Makurdi, babban birnin Jihar Benuwai, sun hana shi shiga jihar a lokacin ziyarar ta’aziyya ga Yelwata.  

Fiye da magoya bayan dan takarar NDC guda 10 sun ji rauni kuma an kai su asibitin koyarwa na jami’ar Jihar Benuwai da ke Makurdi, bayan wannan lamari. 

Yayin da jam’iyyar adawa ta zargi jami’an gwamnati da tallafa wa ‘yan daba, Gwamnatin Jihar Benuwai ta musanta wannan zargi. 

Kusan awa 24 kacal bayan faruwar lamarin, rundunar ‘yansandan Jihar Benuwai ta bayyana cewa ta kama mutum 46 da ake zargi da hannu a harin. 

Jihar Kano 

A ranar 5 ga Satumba, wasu ‘yan daba sun farmaki ‘yansanda da ‘yan jarida a wurin taron jam’iyyar APC a Jihar Kano. 

An kai musu hari a bayan jami’ar arewa maso yamma da ke kofar Nassarawa, yayin da suke kan hanyarsu ta komawa ofisinsu bayan taron. 

An bayar da rahoton cewa masu kai hari sun lalata motar ‘yan jarida kuma sun fasa gilashin baya.  

APC ta gudanar da taron kungiyar goyon bayan Tinubu a filin wasa na Sani Abacha a Kano, inda ta karbi wasu shugabannin jam’iyyun adawa kafin lamarin ya faru. 

An kai harin ne mako guda bayan da aka kashe wani matashi mai suna Yusuf Ahmad a wani harin ramuwar gayya da ‘yan daba suka kai a kan titi rukunin gidaje na Dorayi da ke karamar hukumar Gwale ta jihar. 

A Jihar Kaduna 

A makon da ya gabata, ‘yan jam’iyyar ADC da suka fito don tarbar dan takarar gwamnan jam’iyyar a Jihar Kaduna, Isa Mohammed Ashiru, bayan dawowarsa daga aikin hajji daga Saudiyya sun fuskanci farmaki daga masu tayar da rikicin siyasa. Rahotanni sun nuna cewa wasu motoci na mambobin ADC an lalata su. 

Jam’iyyar adawa ta zargi cewa bayan kai harin, an ga ‘yan daba masu makami suna shiga sakateriyar gwamnatin Jihar Kaduna, wanda ya jawo sabbin damuwa kan tsaron rayuka a lokacin zaben watan Janeru da fabrairu. 

Jihar Ribas 

An sami tashin hankali a wasu sassan Jihar Ribas, musamman a Unguwar Ikwerre da Emohua, bayan rahotannin rikice-rikice tsakanin magoya bayan ADC, NDC da APC. Game da zargin harin da aka kai wa mambobinta da wani dan takara. 

A kwanan nan ADC ta yi gargadi lokacin wani taro a Ikwerre. Haka kuma, a ranar 9 ga Satumba, an ruwaito cewa wasu mutane da ake zargin ‘yan siyasa ne sun mamaye ofishin jam’iyyar NDC a karamar hukumar Emohua, inda suka lalata allunan tallace-tallace da sauran kayan yakin neman zabe na jam’iyyar. 

Jihar Inugu 

Jam’iyyar PDP da kuma NDC sun bayar da rahoton harin da aka kai wa mambobinsu a sassa daban-daban na Jihar Inugu. 

Bayan wasu kwanaki, mutane da dama an ruwaito sun jikkata sakamakon harbin bindiga yayin taron ‘yan jam’iyyar NDC. Wasu daga cikin wadanda abin ya shafa har yanzu suna asibiti a lokacin hada wannan rahoton. 

Jerin hare-haren sun kara haifar da damuwa a fadin kasar game da yuwuwar matakin tashin hankali da za a iya gani kafin, a lokacin, da bayan zaben 2027. 

Da yake zantawa da manema labarai, kwararren masanin tsaro, Mista Donatus Igi ya bukaci hukumomin tsaro da su hanzarta dakile wannan dabi’a kafin zabuka, yana gargadin cewa ta’addancin siyasa na iya raunana gudanar da zabe. 

Ya kawo misalin kisan da ake zargin an yi wa ‘yan jam’iyya da magoya bayansu yayin shirin zaben gwamnan Jihar Osun, inda ake bayar da rahoton cewa fiye da mutane 40 ne ‘yan ta’adda suka kashe. 

A cewar Igi, “Ana samun tashin hankalin siyasa a cikin zabenmu, amma ina ganin a yanzu mun fi jin tsanani.  

Har yanzu ba a fara yakin neman zabe yadda ya kamata ba, kuma mutane da dama ana kai musu hari. Wannan ba dimokuradiyya ba ce. 

“Abin takaici, wasu daga cikin hukumomin tsaronmu an tauye su. Ka duba abin da ya faru a Jihar Osun kwanan nan. An kashe mutane da dama, kuma ‘yansanda da sauran hukumomi suna kallo kawai. A lokuta daban-daban, gwamnan ya yi ihu cewa ‘yansanda suna nuna wariya, amma mutane da yawa sun dauka a matsayin barkwanci. Mun ga abin da ya faru a karshe. 

Siyasa
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Dalilan Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Jinkirta Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

MASU ALAKA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara
Manyan Labarai

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu
Manyan Labarai

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau
Manyan Labarai

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026
Next Post
Siyasa

Idan Kana Da Kyawawan Manufofi A Kan Jihar Gombe, Ka Zo Mu Yi Muhawara — Ɗan Takarar NDC Ga Pantami

LABARAI MASU NASABA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026
Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

October 23, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026
Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

October 23, 2026
Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.