Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa jam’iyyar APC a dunƙule take A Jihar Katsina kuma ita za ta yi nasara a zaɓen 2027Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana haka a wajen taron ƙaddamar da kungiyar yakin neman zaɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tunibu wanda Chief Oweizide Ekpemupolo (Tom Polo) yake jagoranta.
Take yaƙin neman zaɓen dai shi ne “PBAT Door to Door moɓement” inda aka ƙaddamar da kodinatoci ƙananan hukumomi 34 da shugaban ta na jihar Katsina Dakta Faisal Kaita.
A jawabin sa gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa jam’iyyar APC a jihar Katsina guda ɗaya ce, kuma ita ce zata samu nasarar a zaɓen 2027 mai zuwa.Ya ƙara da cewa ya kamata al’ummar Katsina su cigaba da yi wa shugaban ƙasa Bola Ahmad Tunibu godiya saboda irin sauye-sauyen da ya kawo a tsarin tafiyar da gwamnatin Nijeriya shine yake ba su damar shinfiɗa ayyukan alheri da ake gani.
Gwamna Raɗɗa ya ƙara da cewa ya kamata su ci gaba da nuna godiya ga shugaba Bola Ahmed Tinubu, duk da ƴan adawa masu hayaniya da surutu a kafafen sada zumunta suna cigaba da sukar gwamnatin sa”Insha’Allah, za mu kayar da su. za mu yi nasara cikin sauƙi, kuma In Sha Allah, za mu sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekarar 2027.
Gwamnan ya yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce “ina so ka kwantar da hankalinka cewa jihar Katsina jihar ka ce, kuma ba za mu ba ka kunya ba, jam’iyyar APC a guda ɗaya ce, kuma a dunkule take’ Da yake jawabi a madadin wanda ya kafa wannan tafiya, Chief Kestin Ebimorbowei Pondi ya bayyana cewa dangantakar da ke tsakanin shugaban ƙasa da jihar Katsina ce ta gina wannan gaskiyar da amincewa a tsakanin su.
Wakilin Mista Ekpemupolo Tom Polo ya yi kira ga mambobin kungiyar PBAT Door to Door moɓement da su ɗauki sakon wannan gwamnatin zuwa ga ƴan siyasa na ƙasa ta hanyar tattaunawa da al’umma da yan kasuwa da magidanta a ya yin da ake tunkarar zaɓen 2027.














