ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 7, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tallafin Tinubu: Rijiya Ta Ba Da Ruwa Guga Ya Hana

by Sadiq
19 seconds ago

Yayin da gwamnatin tarayya biyan tallafin naira 50,000 ga magidan da ke cikin hali na bukata a duk fadin Nijeriya, mutane da yawa suna tambaya dalilin da ya sa ba su samu kudin ba.

Tallafin, wanda ma’aikatar jinkai rage radadin talauci ta tarayya ke aiwatarwa, an tsara shi ne don taimaka wa magidanta marasa qarfi don su sami sauki ga kuncin rayuwa ta hanyar aika musu da kudi kai tsaye cikin walat din wayarsu ta hannu.

A cewar ka’idojin shirin, wadanda za su amfana za su karbi kudi ta hannun masu ba da tallafin biyan da aka tsara, ciki har da ALAT, MoMo, NairaGram, OPay da Moniepoint.

ADVERTISEMENT

Gwamnati ta ce matakin yana amfani da walat na wayar hannu don tabbatar da cewa tallafin kudi ya isa ga masu cin gajiyarsa cikin sauri kuma a bayyane, tare da auna kansu da ake yi a kowane zagaye na biyan kudi.

Ga bayani kan yadda ake zaben masu amfana da yadda za ka duba matsayinka cikin aminci.

LABARAI MASU NASABA

Abubuwa 6 Da Za Su Iya Haramta Maka Yin Zaɓe A Nijeriya

Matsin Tsadar Rayuwa A Nijeriya: Abubuwa 10 Da Suka Ƙara Tsada A Zamanin Tinubu

Gwamnati ta fayyace matakai hudu ga wadanda aka zaba don samun biyan kudin.-

Ta hanyar karɓar sakon SMS: Za a aika wa wadanda aka zaɓa sakon waya daga daya daga cikin masu bayar da biyan kudi na musamman suna sanar da su cewa an zabe su don cin gajiyar shirin.-

Tabbatar da halarta: Ana bukatar masu karba su amsa da zarar sun sami sakon don nuna cewa sun yarda su shiga shirin.

Jagororin shirin sun bayyana cewa ba za a biya kowane kudi ba sai da amincewar wanda zai amfana.

Sabuntan walat din wayar hannu: Bayan tabbatarwa, za a bude walat din wayar hannu kuma a hada shi da lambar wayar mai amfani da lamban shaidar dan qasa (NIN).

Karba da cire kudin: Za a saka jimillar kudi na naira 50,000 a cikin walat din wanda zai amfana.

Masu karbar kudi na iya cire kudin ta hanyar wakilin POS, a banki ko su kashewa kai tsaye daga aljihun wayarsu.

Masu cin gajiyar za su samu karin umarnin SMS daga masu biyan kudi bayan an qara musu kudi a aljihunsu.

Gwamnati ta bayar da waɗannan lambobin cire kudi kamar haka: ALAT (Wema Bank): danna 94523#.

MoMo PSB: danna 6710#.NairaGram: danna 72600#.

OPay: danna 95520# ko amfani da manhajar wayar hannu.

Moniepoint: danna 557327# ko amfani da manhajar wayar hannu.

A cewar ka’idojin shirin, ana zabar masu cin gajiyar ne ta hanyar amfani da takardun shaidar qasa da na rajistar jama’a ta kasa da aka tabbatar.

Ana tsara tsarin zaben ne don gano magidan talakawa da masu rauni wadanda suka cancanci shiga shirin.

Gwamnati ta bayyana cewa mutane ba za su iya yin aikace-aikace da kansu ko biya don a saka su a jerin masu cin gajiyar ba.

Haka kuma ta fayyace cewa ba kowa za a saka a cikin rukuni na farko na masu cin gajiyar ba.

Gwamnati ta gargadi masu cin gajiyar agajin kudin game da masu yaudara wadanda za su iya kokarin cin gajiyar shirin canja wurin kudi ta hanyar neman kudi ko bayanan bayanan sirri na banki.

Ya ce shirin kyauta ne kuma babu wanda aka ba izinin neman biyan kudi don saukake sakin tallafin naira 50,000.

Jagororin sun jera hanyoyi uku da masu amfana za su iya gane sakonnin shirin na gaskiya: Dole sakoni su zo daga ALAT, MoMo, NairaGram, OPay ko Moniepoint.

Za a tambayi masu karba su amsa su danna lambar USSD da mai ba da kudin ya kayyade kawai.

Sakonni ba za su taba neman biyan kudi ba, lambar sirri (PIN) da OTP ko kuma su karba ta hanyar danna link.

Sai dai kuma gwamnatin tarayya ta ce akwai abubuwan da ya hana wasu ‘yan Nijeriya samun tallafin da suka haɗa da: Rashin shiga cikin rajistar: Don samun cancanta, dole ne mutane su kasance a cikin rajistar, wanda ke dauke da bayanai kan fiye da miliyan 70 na ‘yan Nijeriya.

Waɗanda ba sa cikin wannan rajista ba za su sami tallafin ba.Rashin Cancanta: Shirin bai bayyana sharuɗan rashin cancanta ba, amma ana ba da shawarar cewa mutane na iya rashin cancanta idan ba su cikin rajista ko kuma idan ba su cika ka’idojin talauci da rauni.

Tsokaci kan Lokaci: Wasu kwararru na tambayar lokacin shirin tallafi, musamman yadda yake kusantowa zaben 2027, suna nuna damuwa kan ko wannan wata dabara ce ta siyasa don samun goyon bayan jama’a.

Isasshen Adadi: Akwai damuwa cewa naira 50,000 ba zai wadatar wajen rage matsalolin tattalin arziki da yawancin ‘yan Nijeriya ke fuskanta ba, kuma ko shirin na bayar da tallafin sau daya kawai.

Yana da muhimmanci ga ‘yan Nijeriya su kasance masu samun labarai kuma su tabbatar da gaskiyar duk wani sanarwa game da shirin tallafin don gujewa fadawa tarkon bayanan karya ko zamba.

MASU ALAKA

Rashin Tsaro Na Barazana Ga Zaben 2027 —Rahotanni
Rahotonni

Abubuwa 6 Da Za Su Iya Haramta Maka Yin Zaɓe A Nijeriya

November 5, 2026
Tsadar Rayuwa: Yadda Iyalan Nijeriya Ke Komawa Abinci Mai Rahusa Domin Samun Sauƙin Rayuwa
Rahotonni

Matsin Tsadar Rayuwa A Nijeriya: Abubuwa 10 Da Suka Ƙara Tsada A Zamanin Tinubu

November 4, 2026
Shekara 20 Da Rasuwar Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido
Rahotonni

Shekara 20 Da Rasuwar Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido

November 1, 2026

LABARAI MASU NASABA

Rage Tsadar Rayuwa Ce Babbar Manufarmu – Tinubu

Tallafin Tinubu: Rijiya Ta Ba Da Ruwa Guga Ya Hana

November 7, 2026
Dan Sama Jannati Bako Na Farko Zai Shiga Cibiyar Binciken Sararin Samaniya Ta Sin

Dan Sama Jannati Bako Na Farko Zai Shiga Cibiyar Binciken Sararin Samaniya Ta Sin

November 7, 2026
Yunwa: Ya Kamata ‘Yan Nijeriya Masu Ƙwazo  Su Samu Abinci – Yari

Yunwa: Ya Kamata ‘Yan Nijeriya Masu Ƙwazo Su Samu Abinci – Yari

November 7, 2026
NAHCON Ta Yi Gargaɗi Kan Shafukan Sada Zumunta, Ta Ja Hankali Kan Yaɗa Labaran Karya

NAHCON Ta Yi Gargaɗi Kan Shafukan Sada Zumunta, Ta Ja Hankali Kan Yaɗa Labaran Karya

November 7, 2026
Sojoji Sun Kama Auta Maikyala, Sun Kai Farmaki Maboyar Dogo Gide A Zamfara

Sojoji Sun Kama Auta Maikyala, Sun Kai Farmaki Maboyar Dogo Gide A Zamfara

November 7, 2026
Takarata Ba Ko A Mutu Ko Ai Rai Ba Ce – Gwamnan Kano

Takarata Ba Ko A Mutu Ko Ai Rai Ba Ce – Gwamnan Kano

November 7, 2026
Za Ku Sha Jar Miya A Zangona Na Biyu – Tinubu

Za Ku Sha Jar Miya A Zangona Na Biyu – Tinubu

November 7, 2026
Tinubu Ya Yi Wa Peter Obi Shaguɓe Kan Matsalar Zaizayar Ƙasa A Anambra

Tinubu Ya Yi Wa Peter Obi Shaguɓe Kan Matsalar Zaizayar Ƙasa A Anambra

November 7, 2026
Ba Don Sauye-Sauyen Tattalin Arziƙin Da Muka Yi Ba, Da Darajar Naira Ta Ruguje – Tinubu

Ba Don Sauye-Sauyen Tattalin Arziƙin Da Muka Yi Ba, Da Darajar Naira Ta Ruguje – Tinubu

November 7, 2026
Barazana Ko Tsoratarwa Ba Zai Sa Na Janye Daga Takara Ba – Atiku

Barazana Ko Tsoratarwa Ba Zai Sa Na Janye Daga Takara Ba – Atiku

November 7, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.