Tawagar gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ta isa Bauchi da misalin ƙarfe 1:35 na rana domin halartar jana’izar marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, fitaccen malamin addinin Musulunci da ya rasu jiya.
Jana’izar za a yi ta da misalin ƙarfe uku na yau Juma’a a babban filin Idi na Bauchi, inda ake sa ran dubban mutane za su hallarci taron addu’ar da za a yi wa marigayin.
- Tawagar Atiku Ta Isa Bauchi Don Halartar Jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi
- Sheikh Zakzaky Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
A cikin tawagar da ta wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu akwai gwamnoni, da ministoci da manyan jami’an gwamnati irin su Ministan Lafiya Ali Pate, da Ministan Harkokin Waje Yusuf Tuggar, da sanatoci ciki har da Sanata Shehu Buba. Haka kuma tsohon gwamnan Bauchi, Ahmadu Mu’azu, shi ma ya na cikin tawagar.
Gwamnan Bauchi Bala Mohammed tare da gwamnonin Kano da Neja ne suka karɓi tawagar a filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa, na Sir Abubakar Tafawa Balewa. Rahotanni sun nuna cewa tun da safiyar yau jama’a daga sassa daban-daban na ƙasar suke ta tururuwa zuwa Bauchi domin halartar jana’iza da yin ta’aziyya ga mabiyan Darikar Tijjaniyya da masoya marigayin Sheikh Dahiru Bauchi.















