ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinkarar Kalubalen Duniya Ta Hanyar Haɗin Gwiwar Aikin Gona Na Shawarar Ziri Ɗaya Da Hanya Ɗaya

by CGTN Hausa
3 years ago
Duniya

Tun daga shekarar 2013, ƙasar Sin ta hanyar shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya” ko BRI a taƙaice, wanda shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya gabatar, da nufin ƙarfafa ababen more rayuwa, da cinikayya da zuba jari, ta ƙulla haɗin gwiwa a fannin aikin noma tare da ƙasashe da dama da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa daban-daban, kawo yanzu, ta ƙulla yarjejeniyoyin haɗin gwiwa a fannin aikin noma da ƙasashe da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa sama da 90, kuma ta gudanar da ayyukan zuba jari a aikin noma sama da 650 a ƙasashen abokan hulɗar BRI da darajar ta kai dalar Amurka biliyan 14.  

Tun lokacin da aka gabatar da shawarar, wato haɗin gwiwar aikin gona na BRI, ya ƙarfafa ayyukan ƙasa da ƙasa da ma na duniya da aka jinginawa kawar da shingayen ci gaba a fannin aikin gona da samar da ababen more rayuwa gami da ingantacciyar hanyar sufuri don jigilar amfanin gona zuwa kasuwanni, da inganta haɗin gwiwar bincike a fannin kimiyyar aikin gona da inganta rumbunan ajiyar hatsi da ban ruwa da sauransu, tare da gabatar wa manoma yadda ake gudanar da ayyukan noma na zamani da kayan fasaha waɗanda ke sauƙaƙa aikin noma da haɓaka aikin noma mai ɗorewa.

  • CMG Ya Hada Gwiwa Da Kafofin Yada Labaru Na Kasashen Da Ke Bin Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”
  • Jiragen Kasa Dake Tafiye-Tafiye Kan Yankin Ciyayi Na Pampas

Bugu da ƙari, a cikin shekaru 10 da suka gabata, ƙasar Sin ta tura kwararrun masana aikin gona sama da 2,000 zuwa ƙasashe sama da 70, tare da koyar da su fasahohin noman shinkafa, da na leman kwaɗo da dai sauransu. A cikin wannan lokacin, an horar da manoma sama da 100,000 kuma sama da miliyan 1 sun samu tallafin kai tsaye don magance matsalolin da manoma da ma’aikata daban-daban suke fuskanta a tsarin darajar abinci. A sa’i daya kuma, a dukkan matakai guda hudu na tsarin tabbatar da wadatar abinci wanda ya kunshi ayyukan samar da kayayyakin amfanin gona, da suka hada da samar da iri da shuka, da sarrafa su, da kuma isar da amfanin gona ga abokan cinikayya, ƙoƙarin da ƙasar Sin ta jagoranta ya tinkari ƙalubalen da aka shafe shekaru da dama ake fama da su, waɗanda suka kawo cikas ga bunkasuwar fannin aikin gona da masana’antu masu alaƙa.

ADVERTISEMENT

A yawancin ƙasashe masu ƙananan ƙarfi da masu matsakaitan kuɗin shiga, inda akasarin ma’aikata suka tsunduma cikin aikin noma wanda ya kasance sama da kashi 25 cikin 100 na GDPn su, haɗin gwiwar aikin gona na BRI mai nasaba da musayar fasahohin noma da zuba jarin noma, da zuba jari a ayyukan samar da ababen more rayuwa da kuma hanzarta daidaita manufofin siyasa, yana baiwa wadannan ƙasashe masu tasowa, waɗanda ke fama da kalubalen tsarin, wata dama ta musamman na samun ci gaba mai ɗorewa ta hanyar noma, da shiga sabbin kasuwanni da manyan kasuwanni, da ƙarfafa samar da ayyukan yi, da inganta samar da abinci.

Hakazalika, haɗin gwiwar aikin gona na BRI, musamman ga ƙasashen da ke yankuna masu fama da talauci ya zama rigakafin manyan ƙalubalen da ke kawo cikas ga samar da abinci da kawar da fatara. Duk da cewa a halin yanzu, haɗin gwiwar aikin gona na BRI na da jerin nasarorin da aka samu a duk fadin ƙasashen Afirka da Asiya, ƙoƙarin da ƙasar Sin ke jagoranta zai iya ƙara inganta samar da abinci a duniya, da kawar da matsanancin talauci ta hanyar faɗaɗa haɗin gwiwar da sauran ƙasashen duniya.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

A watan Oktoban nan ne ake sa ran taron haɗin gwiwa tsakanin ƙasa da ƙasa karo na uku na shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya” zai haɗa ƙasashe da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da kuma bikin cika shekaru 10 da kafa ƙungiyar BRI.

Taron zai zama wata muhimmiyar hanya ga masu tsara manufofi, abokan raya ƙasa, da sauran masu ruwa da tsaki, don yin musayar kwarewa, da buɗe sabbin damammaki na samun bunƙasuwa a ƙarƙashin ƙoƙarin da ƙasar Sin ke jagoranta na tinkarar ƙalubalen duniya. (Muhammed Yahaya)

Duniya
CGTN Hausa
+ postsBio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
NNPCL

Babu Maganar Dawo Da Tallafin Man Fetur -  NNPCL

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.