Daniel Bwala, mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan yaɗa manufofi, ya ce gwamnatin tarayya ba za ta tattauna da ’yan ta’adda ba.
A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, Bwala ya ce gwamnatocin baya sun kan tattauna da ’yan bindiga ne kawai idan rayukan mutane na cikin hatsari.
- Sin Da Rasha Sun Yi Shawarwari Kan Manyan Tsare-tsaren Tsaro
- Yadda Tinubu Ya Naɗa Tsohon Shugaban Rundunar Tsaro Christopher Musa A Matsayin Sabon Ministan Tsaro
Ya ce akwai wani tsari da ya bai wa gwamnati damar tattaunawa domin ceton rayuka.
Sai dai Bwala ya ce hakan ta ƙare.
“Gwamnatin tarayya ba za ta tattauna ba,” in ji shi.
Ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya kawo ƙarshen tattaunawa saboda biyan kuɗin fansa ko yarjejeniya na iya ƙara wa ’yan ta’adda ƙarfi.
Bwala ya ƙara da cewa ba duk sako mutane da aka yi ke da alaƙa da kuɗi ba.
Wani lokaci limamai ne suke shiga tsakani, wani lokaci jami’an tsaro suna matsawa ’yan ta’adda, ko kuma su ’yan ta’addan su yanke shawarar sako mutane.
Ya kuma musanta jita-jitar da ke cewa ana matsa wa Tinubu ya yi murabus.
“Babu wanda ke cikin gwamnati da yake kiran Shugaba Tinubu ya yi murabus,” in ji shi.














