A karshen makon jiya ne Editanmu Bello Hamza ya tattauna da Kwamared Bishir Dauda a kan halin da kasa ke ciki da kuma yadda yake ganin shugaban kasa Bola Tinubu ke tafiyar da mulkin Nijeriya, musamman yadda yake tunkarar matsalalolin tsaro da kuma tsangwamar da Amurka ke yi mana a kan zargin yi wa Kiristoci kissan kare dangi. Ga dai yadda hirar ta kasance.
Za mu so ka gabatar mana da kanka
- Wang Yi Ya Zanta Da Ministocin Wajen Cambodia Da Thailand
- FIFA Za Ta Bayar Da Dala Miliyan 50 Ga Kasar Da Ta Lashe Gasar Cin Kofin Duniya
Sunana Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina, dan rajin kare Dimokaradiyya, hakkin dan Adam da ganin dunkulewar kasashen Afirika. Ina jagorantar kungiyar farar hula mai suna ‘Citizens Participation Against Corruption Initiatibe’, kuma nine babban sakataren Kungiyar Muryar Talaka a Nijeriya.
Kwanan nan Shugaba Tinubu ya sanya dokar-ta-baci a bangaren tsaro a kasar nan, wani karin bayani zaka yi a kan haka.
Shugaba Tinubu yana ta kara ba makiyan Nijeriya mamaki. Yana nuna kwarewa da gogewa a sha’anin mulki fiye da tunanin duk mai tunani. Sanya dokar ta-baci sako ne ga makiyan Nijeriya na cikin gida da na waje cewa gwamnati ba barci take ba. Kuma shugabanninmu ba su rude ba. Suna daukar matakai dalla-dalla don tunkarar kowane irin kalubale ko barazana da ke fuskantar kasar nan. Kada ka manta kasarmu na fuskantar barazana daga shugaban wata kasar waje wadda keda tarihin yi wa kasashe katsa-landan. Amerika karkashin Donald Trump ta samu matsala. Ba su girmama dawaici da mutuncin wasu kasashe. Sannan Donald Trump babu ruwan shi da dokokin kasashen duniya, babu difilomasiyya ko dattako a harkar shi don haka dole shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci. Fatanmu shi ne jami’an tsaronmu a daidai wannan mawuyancin hali da muke ciki za su nuna matukar kishin kasa ta hanyar nuna sadaukarwa. Su yi koyi da takwarorin su na kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso wanda suke aiki da kishin kasa ba tare da nuna gazawa ba.
Yakamata ‘yan siyasa masu siyasa da tsoro da su daina. Nijeriya ce farko kafin siyasa. Sai akwai Nijeriya kafin a yi siyasa.
Haka muma farar hula ya kamata mu saita kanmu. Yanzu muna fuskantar wani irin kalubale, to ya kamata mu hada kai da gwamnati mu kare mutuncin kasarmu. Jayayya a daidai wannan lokacin hadari ce mu guje ta.
‘Yan Nijeriya da dama sun yaba da nadin Janar CG Musa a matsayin Ministan Tsaro. Wani tasiri kake ganin haka zai kara wa harkar samar da tsaro a Nijeriya?
Shugaba Tinubu ya jefi tsuntsaye da yawa da dutsi daya. Na farko ya rufe bakin ‘yan ta tarwatse masu cewa ana ma Kiristoci kisan gilla. To yanzu Kirista ne Ministan Tsaro. Zai yiwu Ministan Tsaro Kirista ya bari ana ma ‘yan uwanshi kiristoci kisan gilla? Na biyu, Shugaba Tinubu ya rufe bakin masu cewa yakamata a nada tsohon soja a matsayin Ministan Tsaro. To yanzu ga shi ya nada tsohon soja a wannan mukami. Na uku, nadin CG Musa kariya ce ga gwamnatin da mulkin Dimokaradiyya, idan mu kai la’akari da yadda sojoji ke hambarar da gwamnatoci a kasashen Afirika. CG Musa ya san sojoji, yasan matsalolinsu don haka, yana da ilimin abin da zai dakike duk wani yunkuri da za a iya yi don illata Dimokaradiyya. Idan ka hada da tsaffin sojojin da Tinubu ya nada jakadoji, yanzu gwamnatin na cike da sojoji ta yadda an kara rufe bakin masu ganin sojoji nada hujjar yin kutse.
To sai dai CG Musa ba zai iya samun cikakkiyar nasara ba, sai ya yi aiki hannu da hannu tare da ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan Tsaro, dama gwamnoni. Maganar ba zai tattauna da ‘yan ta’adda ba, yakamata ya je yai shawara da sauran masu ruwan da tsaki.
Wani kira kake da shi ga al’ummar Nijeriya na su ba gwamnati goyon baya don samun nasarar samar da tsaro a fadin kasar nan?
Gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah. Yanzu an yo walkiya an ga kowa. Masu kai kasarmu kara zuwa ga Amerika da kiran ta kawo mamu hari, suna da sauran mantuwa. Watakila basu ma bibiyar abubuwan da ke faruwa a duniya. Babu wata kasa da za ta iya gyara Nijeriya. A tarihi ba a taba samun wata kasa ta je ta gyara wata kasa ba. Kila hakan yasa mutanen kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso suka kori sojojin kasashen Yamma. Duk wanda yake tunanin Amerika za ta zo ta taimakai to bai ma fahimci Amerika ba. Hawan Donald Trump, Amerika ta soke hukumar I SAID mai bada tallafi. Ta soke tashar rediyon Hausa ta BOA, ta soke shirin AGOA, sannan Amerika ta koma tana lafta wa kasashenmu harajin cinikayya. To Yaya me yin haka zai taimake ka in banda batan basira?
Mu hada kai da gwamnati ya zama wajibi. Mun ga yadda ‘yan Nijar suka hada kai da gwamnatin mulkin soja suka hana kungiyar ECOWAS katabus. To in har wasu duk da mugunta irin ta mulkin soja, amma saboda kishin kasa, za su hada kai da sojan, me zai sa muda keda shugaba adali wanda muka zaba ba za mu hada kai da gwamnati ba?
Ko akwai wani bayani da kake son yi wa al’umma wanda bamu tabo ba?
Yakamata ‘yan Nijeriya mu kalli baiwar da Allah ya yi mana, mu gode mai, mu so kasarmu. Mu daina kira wa kanmu ruwa. ‘Yantawaye da masu tada tarzoma su daina. Ba in da tsiya da bindiga za sui kai mutum. Duk irin rashin mutuncin mutum kafin shi an taba wani, Kuma Allah ya kauda shi. Saboda haka mu bi a hankali mu saita kasarmu. Kada mu yarda mu raba kawunanmu, kasashe ‘yan mamaya su samu damar cimmamu.
Mun gode kwarai da gaske
Nima na gode














