Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙalubalanci masu neman shugabancin Nijeriya da su san me za su iya aiwatarwa kafin su bayyana, na daga batun kuɗaɗe ta yadda za a samar da su, da kuma ɗorewar su.
Tinubu ya ce dole ne kowane alƙawari da gwamnati ta ɗauka ya kasance yana da ingantaccen tsari da kuma hanyar samar da kuɗin aiwatar da shi mai ɗorewa, domin kauce wa ɗora nauyi a kan ’yan Nijeriya da al’ummomin da za su zo nan gaba.
Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, inda ya jaddada cewa dole ne shugabanni su daidaita buƙatar sauƙaƙa wa jama’a rayuwa a halin yanzu da kuma nauyin kare makomar ’yan ƙasar.
A cewarsa, “ɗaya daga cikin nauyin da ke kaina a matsayina na Shugaban Ƙasa shi ne samar da sauƙi ga jama’a a yau, ba tare da lalata makomar ’ya’yanmu ba.
“Dole ne kowane alƙawari ya kasance mai ɗorewa kuma ya dogara da ingantaccen tsari. Wannan nauyin ne ke jagorantar shawarwarin da muke yankewa, ciki har da waɗanda suke da wahala.”














