Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce tsananin matsin tattalin arziki, rashin aikin yi da tsadar rayuwa na tura matasan Nijeriya shiga sana’o’in da ke da haɗari domin neman abin dogaro da kai.
Atiku, wanda ya bai wa iyalan mutane 37 da suka mutu a hannun Rundunar NSCDC a Minna, Jihar Neja, tallafin naira miliyan 20, ya bayyana hakan ne yayin ganawa da iyalan mamatan da kuma wadanda suka tsira daga lamarin.
Ya ce mutuwar matasan ya kamata ta zama dalilin gudanar da bincike mai zurfi kan matsalolin talauci, rashin aikin yi da tsadar rayuwa da ke tilasta wa matasa ɗaukar irin waɗannan kasada.
Ya kuma bukaci a tabbatar da gaskiya, adalci da daukar matakin da ya dace kan abin da ya faru, yayin da gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin mutum 10 domin binciken musabbabin mutuwar mutane 37 da ke tsare a hannun NSCDC.
Atiku ya ce kamata gwamnati ta samar wa matasa ilimi, dabarun sana’a da ayyukan yi domin su samu damar gudanar da rayuwa ta hanyar da ta dace, maimakon shiga ayyukan da ke jefa rayukansu cikin haɗari.














