Sulaiman Ibrahim" />

Tsaro: Wasu Gwamnonin Nijeriya Na Ganawa Da Shugabannin Fulani Makiyaya

Yau gwamnonin yammacin Nijeriya ke gudanar da wani taro da shugabannin kungiyar Fulani makiyaya sakamakon tankiyar da ta biyo bayan umurnin ficewar su daga Jihar Ondo kamar yadda Gwamnatin Jihar ta basu umurni cikin mako guda.
Rahotanni sun ce yanzu haka shugabannin kungiyar Miyetti Allah sun isa Akure domin halartar taron wanda zai samu halartar Gwamnan Jigawa da Kebbi da kumą kwamishinonin Yan Sandan dake Yammacin Nijeriya.

Sakatare Janar na kungiyar Meyetti Allah Baba Usman Ngelzerma ya tabbatarwa RFI Hausa isar su Akure yammacin jiya, domin halartar taron.

Umurnin da aka yiwa Fulanin na ficewa daga Jihar Ondo da kuma harin da aka kaiwa Sarkin Fulani a Jihar Oyo sun tada hankalin jama’a inda aka dinga samun musayar zafafan kalaman dake iya raba kań jama’a’r Nijeriya.

Exit mobile version