Kafafen yada labaran kasar nan sun cika da rahotanni kala-kala kwanan nan inda suka bayyana cewa, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kaddamar da wasu tsare-tsare da za su dakatar da ficewar da Likitoci, ma’aikatan lafiyar Nijeriya ke yi zuwa kasashen waje.Ana ganin wannan wani martani ne na yadda aka cigaba da samun Likitocin Nijeriya ke tserewa zuwa kasashen waje domin samun rayuwa ta-gari da albashi mai tsoka musamman a kasashe irinsu Amurka, Turai da kuma Saudiyya.
Wadannan sabon tsare-tsaren da gwamnati ta fito da su, sun yi hannun riga da manufar gwamnati a baya, inda ta ke karfafa likitoci su fita zuwa kasashen waje domin neman ingantacciyar rayuwa ta kansu da iyalansu. Saboda wannan tsarin ne, Farfesa Isaac Adewole, wanda shi kan shi farfesa ne na harkar lafiya kuma tsohon shugaban jami’ar Ibadan ne, a lokacin yana Ministan Lafiya a karkashin gwamnatin Muhammadu Buhari, ya taba yin kira ga Likitocin Nijeriya da su rungumi aikin noma a matsayin wata hanyar nishadantar da kan su da kuma matsayin maganin kukan da suke yawan yi na rashin isasshen albashi da sauran alawu-alawus.
- Binciken LEADERSHIP Hausa… Asalin Abin Da Ya Faru Da Iyalan Da Suka Mutu Sanadin Gurbataccen Abinci
- Yadda Al’ummar Da Ke Zaune Da ‘Yan Bindiga Ke Rayuwa A Zamfara
Bayan wannan katobarar, sai gashi kuma wani minista a gamnatin na Muhammadu Buhar, ministan kwadago, Dr Chris Ngige, wanda shima likita ne,ya yi ikirarin cewa, NIjeriya na da isasshun likitoci da za su iya bai wa wasu kasashen rarar likitocin da suka rage, amma kuma hakikanin gaskiya ba haka lamarin yake ba.Hakanan shi ma mai ba shugaba Buhari shawara a bangaren harkar yada labarai, Femi Adesina, ya goyi bayan wadannan shawarwarin inda ya ce, shi bai ga matsalar da fitar likitocin take haifarwa ba, domin kuwa hakan na taimakawa wajen kara kwarewar likitocinmu su samu irin kwarewar da ba za su iya samu a cikin Nijeriya ba.
In har za a yi wa wadannan jami’an gwamnatin adalci, lalle babu wani laifi ga ma’aikatan lafiya su nemi wata hanyar gudanar da rayuwa baya ga harkar da suka samu horo a kai ta likitanci. Musamman ganin an taba samun wani shugaban bankin duniya mai suna Jim Yong Kim, wanda babban likita ne shaharre.A gwamnatin Buhari, Okechukwu Enelamah wanda ministan ciniki da zuba jari ne amma kuma cikakken likita ne da ya fada cikin harkokin kasuwanci. Amma kuma abin da ya kamata a lura a nan shi ne wadannan sun kauce wa harkar kiwon lafiya ne a matsayin zabin kansu ba wai sun kauce ba ne sadoda rashin jin dadin aiki a matsayin likita a Nijeriya.
A ra’ayinmu, wadannan maganganun na manyan kuma jami’an gwamnati su ne manyan dalilan da suka sa likitocin Nijeriya suka fara kaura zuwa kasashen waje. A tsokacinsa, Sakataren Gwaamnatin tayarayya a zamanin mulkin Shugaba kasa Buhari, Boss Mustapha, ya bayyana cewa bai san tsananin karancin likitoci a kasar nan ya kai lamarin da ya gani ba a lokacin cutar Korona.A kan haka ya fahimci cewa, lalle ya kamata a dauki matakan dakile ficewar likitocinmu da suke yi zuwa kasashen waje.
Kamar dai sauran bangarorin rayuwar Nijeriya, mahukunta sun yi watsi da harkar kiwon lafiya da yadda ake gudanar da ita a asibitocinmu, sun yi watsi da yadda ake gudanar da harkokin kula da lafiyar al’umma a asibitoci.Wannan kuma da gangan ne suka yi hakan domin wadannan mahukunta na tafiya kasashen waje ne domin kulawa da lafiyar su da ta iyalansu,wannan matakin kuma ya taimaka wajen tsotse kudaden ajiyar kasa na kasashen waje. Cin hanci da rashawa sun taimaka wajen tatse kudaden da aka ware domin kulawa da bangaren kiwon lafiya.
Ta haka ne kayan aiki na zamani suka yi karanci a asibitocinmu,inda harkar kiwon lafiya ta koma bangaren masu zaman kansu, inda su kuma suka dora ta, a harkokinsu saboda neman riba, hakan kuma ya sa talakawan da basu da kudi daga samun ingantacciyar kiwon lafiya saboda rashin kudi.
A bayyane lamarin yake,a wasu lokutta, Likitoci a asibitocin gwamnati zaka ga suna sayen safar hannun wadda suke amfani da ita wajen duba marasa lafiya.Duk da muhimmancin wadannan kayan aiki ba a samu a asibitoci domin amfani Likita. Wannan kadai sun isa ya ba mutum cikakken sanin halin da fannin lafiya yake ciki.A ra’ayinmu karin abin da ke kara mastalar da Likitocin Nijeriya suke fuskanta su ne yawan aiki da kuma rashin ingantacen albashi.Halin tabarbarewar asibitocin Nijeriya ya ke karfafa masu karbar aiki daga kasashen waje da zarar an yi masu tayi.
Daga wadannan hujjojin ne, muka yi garo da duk wani mataki na hana Likitoci cika burinsu na aiki a wasu wuraren domin sun yi karo da dokokin kasa da na kasashen waje, wadanda suka samar da ‘yancin rayuwa a ko’ina a fadin duniya matukar mutum ya cika ka’idojin da aka tsara.Sai dai irin likitocin nan da gwamnnati ta horas ta kuma shiga wata yarjejeniya da su, in ba haka ba, to haramun ne neman dakatar da kowa, ba ma Likitoci kawai ba daga fita kasashen waje don neman ingantacciyar rayuwa.
Maimakon sanya wasu dokokin da za su takura fitar Likitoci kasashen waje, ya kamata gwamnati ta lura da bangarorin da ke bukatar gyara domin ta inganta su musamman abin da suka shafi kayan aiki albashi da jin dadin likitoci gaba daya da kuma kudaden giratuti in Likita ya bar fagen aiki.
Hakanan kuma dole gwamnati ta dakatar da shirin nan na tura manyan jami’anta kasashen waje domin duba lafiyarsu. Kudaden da ake zubawa domin wannan tafiyar neman lafiya sai a tura su domin samar da cikakkun kayan aiki a asibitocinmu