Turkiyya ta bude sansanin sojinta mafi girma a kasar waje a birnin Mogadishu babban birnin ƙasar Somaliya, a wani bikin da shugabannin Somalia da manyan jami’an soji da na diplomasiyyar ƙasar ta Turkiyya suka halarta.
Fira Ministan Somalia Hassan Ali Khaire da shugaban rundunar sojin Turkiyya, Janar Hulusi Akar sun kaddamar da sasanin soji mafi girma da Turkiyya ta gina a Mogadishu. Sansanin mai tsawon kilomita huƙu, na ƙauke da ƙakunan kwanan sojoji da wurin horo da na motsa jiki.
An kwashe shekaru biyu ana gina wannan sansanin wanda aka kaddamar da shi a jiya Asabar. A cewar Janar Akar, bude wannan sansanin da ƙasar Turkiyya ta yi, alama ce da ke nuna yadda ƙasar ta himmatu wajen taimakawa Somalia. Fira Minista Khaire ana shi bangaren ya ce, bude sansanin wata alama ce da ke nuna cewa Somalia ta dauki hanyar kare kanta. Sama da dakarun Turkiyya 200 za su horar da takwarorinsu na Somalia sama da 10,000, a cewar ma’aikatar tsaron Somalia a wannan sansanin. Sansanin sojin da aka buƙe shi a jiya Asabar, bayan kammala gininsa a kan dala miliyan 50, shi ne mafi girma da Turkiya ta taba budewa a wata kasa.
Kazalika kwamandan ya ce za’a iya horar da sojoji dubu daya a lokaci guda cikin sansanin ba tare da matsi ba. Matakin ya daƙa ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu musamman ta fuskar dilfomasiya da kuma tsaro, kasancewar buƙe sansanin ya zo a dai-dai lokacin da ƙasar ta Somalia ke fama da hare-haren mayaƙan ƙungiyar al-Shebaab da ke neman hambarar da gwamnatin ƙasar.