Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
Shirin kasar Amurka na USAID za ta kashe kimanin Dalar Amurka Miliyan 60 a jihohi biyar da suke Nijeriya domin tabbatar da samar da tsaftataccen ruwan sha da na amfanin yau da gobe a cikin shirin nan na ‘USAID Water, Sanitation and Hygiene (WASH).’ Shugaban shirin USAID na inganta sha’anin ruwan sha da na amfani, Mr. Timeyin Uwejamomere ne ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki na kwana uku da aka gudanar a Bauchi.
Mr. Timeyin Uwejamomere ya ce wannan shirin na Hukumar USAID zai taimaka ta fuskacin inganta kiwon lafiyar al’ummar Nijeriya da kuma samar musu da ingantacce, gami da tsaftataccen ruwan da za su rika amfani da shi na yau da gobe.
A cewarsa, wannan shiri na gwaji zai gudana ne a jihohin Bauchi da kuma Kaduna domin tabbatar da al’umma mazauna yankunan karkara suna samun ingantaccen ruwan sha da na amfanin yau da gobe da suke amfani da shi gami da samun tsaftataccen muhalllin da za su rika rayuwa domin samun al’umma masu ingantaccen lafiya.
Ya ce, hakan zai taimaka wajen hadaka da Hukumomin ruwa na jihohin domin tabbatar da ruwan da jama’a ke sha mai tsafta da inganci ne domin samun al’umma masu kosasshen lafiya a kowane hali.
Shugaban shirin na WASH ya kuma jinjina wa kokarin G jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar a bisa domin rattaba hannu da ya yi kan shirin na WASH da kuma amincewarsa kan hakan.
Tun da farko a jawabinsa, shugaban Hukumar ruwa na jihar Bauchi, Injiniya Aliyu Aminu Gital ya bada tabbacin gwamnatin jihar Bauchi za ta bada cikakken goyon baya wa shirin USAID domin tabbatar da samar da ruwa mai nagarta da jama’a za su rinka amfani da shi a kowane lokaci.
Ruwa dai kamar yadda aka sha nanatawa, abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar kowace al’umma, a kowane janibi, ruwa abu ne wanda ya zama dole a yi amfani da shi. A bisa haka ne kungiyoyi ke kokarin tabbatar da inganci da kuma samar da shi ga jama’a cikin birni ko na karkara. Ya zuwa yanzu dai wasu yankunan jihar ta Bauchi suna fama da matsalolin rashin ingancin ruwa a bisa haka ne ake ganin wannan shirin zai taimaka matuka gaya wa sashin ruwan da kuma tabbatar da ingancin domin samun al’umma masu kosasshen lafiya kamar yadda masanan suka yi nazari.