ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

WAEC Na Buƙatar Kwaskwarima

by Alhaji Adamu Rabiu
6 months ago
WAEC

Bayan shekaru 73 da kafuwarta, Majalisar gudanar da Jarrabawar Afirka ta Yamma na bukatar yi mata garanbawul cikin gaggawa. Matsalolin da dalibai suka fuskanta a wasu cibiyoyi a lokacin jarrabawar kammala sakandare ta 2024/25 na nuni da koma bayan da WAEC ke fuskanta da kuma bukatar a yi mata kwaskwarima ga ayyukanta.

Biyo bayan fitowar takardar tambayar harshen turanci kwanaki hudu kacal kafin a fara jarrabawar, majalisar ta tilasta sake buga tambayoyin. Hakan ya sa dalibai suka zauna jarabawar har cikin dare. Lokacin da fitilun suka mutu, dalibai sun koma amfani da tocila, kyandir, da kowace irin fitila a madadin hasken lantarki. A wata cibiya wani rufi ya kusa fadowa kan wasu daga cikin zaliban.

  • Bayan Biyan Basussuka: WAEC Da NECO Sun Saki Samakon Jarrabawar Jihar Zamfara
  • Gwamnatin Tarayya Ta Umurci WAEC, NECO Su Koma Amfani Da CBT Nan Da 2026

Lamarin dai ya jefa firgici a gidaje da dama, inda iyayen da masu kulawa suka fusata suka yi ta kiraye-kirayen kare lafiyarsu da kuma inda ‘yan uwansu suke. Rahotanni sun ce wasu jami’an hukumar ta WAEC na karkashin ‘yansanda suna binciken lamarin, wanda ya shafi cibiyoyi a Legas, Ogun, Osun, da Taraba.

ADVERTISEMENT

An kafa WAEC ne a shekarar 1952 don gudanar da jarrabawar a Nijeriya da wasu kasashe hudu na yammacin Afirka da ke magana da Ingilishi, Ghana, Saliyo, Laberiya, da Gambiya, tare da ba da izinin bayar da takaddun shaida kwatankwacin daidaikun hukumomin da ke yin jarrabawar a duniya.

Hukumar ta taka rawa daidai da yadda da ake tsammani shekaru kusan ashirin bayan kirkirar ta. Jarrabawar ta zarce yadda aka yi zato, domin na gyara rayuwar miliyoyin dalibai da suka zama kwararru, shugabannin kasa, da manyan abin alfahari a duniya a fagage daban-daban.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Karɓa Ko Sauyawa Ɗalibai Aji Kai Tsaye Zuwa SS3

Obi Ya Yi Alkawarin Biyan Kudin Jarrabawar NECO Na Fursunoni 148

Duk da haka, a cikin ‘yan shekarun da suka wuce, rashin daidaituwa na jiki ya bayyana. Jami’ai sun fara fitar da takardun tambayoyi domin samun kudi a wasu kwanaki kafin a fara jarabawar, inda ‘yan kasuwa marasa kishi, dillalai, da malalata dalibai suka lalata shirin.

Wannan ya gurgunta kyawawan manufofin WAEC da ta bada fatawa da kuma kawo cikas ga ingancin takaddun shaida.

Abubuwan da suka faru na baya-bayan nan sun kara jaddada lalacewar tsarin ilimin kasar. Kusan wata guda da fitowar WASSCE, matsalar tsara JAMB ta tilasta wa dubban daliban UTME a jihohi shida da wasu sassan Legas yin jarrabawar bayan an basu maki kadan.

Wannan abin takaici ya sa wata daliba da abin ya shafa ta kashe kanta a Legas, sai dai daga baya hukumar ta JAMB ta yarda cewa babbar matsalar da aka samu gazawarta ce ba ta dalibai ba.

Shekarar 1970 ta kawo sauyi a koma bayan WAEC. Badakalar Owosho, inda wani jami’in hukumar ya fallasa amsar da dalibai suka yi a gaban jarrabawar, ya sa aka soke jarabawar a wasu cibiyoyi, wanda ya tilasta wa wadanda suka yi laifi da wadanda ba su ji ba gani ba su ci jarrabawar a shekara mai zuwa tare da kananan yaransu. Sai dai, sulhun da aka yi a shekarar 1977, wanda aka yi wa lakabi da ‘Edpo’ 77’, ya rufe rugujewar Owosho ta kowace fuska.

Dole ne WAEC ta fanshi kanta ta hanyar toshe madogarar da ma’aikatan da ba su da gaskiya suke ba da takardar tambayar ta. Dole ne ta gano tare da mika miyagu ga ‘yansanda domin gurfanar da su gaban kuliya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Karɓa Ko Sauyawa Ɗalibai Aji Kai Tsaye Zuwa SS3
Ilimi

Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Karɓa Ko Sauyawa Ɗalibai Aji Kai Tsaye Zuwa SS3

December 14, 2025
Obi Ya Yi Alkawarin Biyan Kudin Jarrabawar NECO Na Fursunoni 148
Ilimi

Obi Ya Yi Alkawarin Biyan Kudin Jarrabawar NECO Na Fursunoni 148

December 14, 2025
Fadar Shugaban Kasa Ta Karrama Daliban Da Suka Nuna Hazaka A 2025
Ilimi

Fadar Shugaban Kasa Ta Karrama Daliban Da Suka Nuna Hazaka A 2025

November 30, 2025
Next Post
Yunwa Da Talauci Ne Ke Barazana Ga Harkar Tsaro A Kasar Nan — NSA, CDS

Yunwa Da Talauci Ne Ke Barazana Ga Harkar Tsaro A Kasar Nan — NSA, CDS

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.