A daren 28 ga wannan wata ne, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya tattauna da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden ta wayar tarho, inda ya yi bayani kan nauyin da ke bisa wuyan kasashen Sin da Amurka, ya kuma yi nuni da cewa, Amurka ta yi kuskuren fahimtar dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka da kuma bunkasuwar kasar Sin, sa’an nan ya bayyana matsayin kasar Sin kan batun Taiwan.
A nasa bangaren, Biden ya bayyana fatansa na neman hada kai a tsakanin Amurka da Sin, da daidaita sabani yadda ya kamata, ya kuma yi alkawarin cewa, Amurka ba ta sauya kuma ba za ta sauya manufar “kasar Sin daya tak a duniya” ba, ba kuma ta goyon bayan ‘yancin Taiwan.
Wannan ne karo na 5 da shugabannin Sin da Amurka suka tattauna da juna ta wayar tarho, tun bayan Biden ya zama shugaban Amurka.
Kana kuma, tattaunawar da shugabannin 2 suka yi a wannan karo, tana da matukar muhimmanci a wannan muhimmin lokaci. Yanzu haka yaduwar annobar cutar COVID-19 da rikicin Ukraine sun kawo tsaiko ga batutuwan ci gaba da kuma tsaro.
Yayin da kasashen duniya suke fuskantar sauye-sauye da matsaloli, suna fatan Sin da Amurka za su daidaita sabanin dake tsakaninsu yadda ya kamata, za kuma su ba da jagora wajen kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya da kara azama kan bunkasar duniya.
An lura da cewa, a wannan karo, shugaba Xi ya mai da hankali wajen yin bayani kan matsayin kasar Sin game da batun Taiwan, wanda shi ne mafi muhimmanci da kuma jawo hankali a fannin huldar da ke tsakanin Sin da Amurka.
Baya ga haka, a halin yanzu ana kara fuskantar barazana a mashigin tekun Taiwan sakamakon wutar da Amurka take ta rurawa.
Wajibi ne Amurka ta fahimci cewa, idan ba ta tinkari batun Taiwan yadda ya kamata ba, to, za a yi illata huldar da ke tsakanin Sin da Amurka, wadda ba a taba ganin irinta ba.
Amurka ta sha yin alwashin martaba manufar “kasar Sin daya tak a duniya”, da rashin goyon bayan ‘yancin Taiwan, to, wajibi ne ta cika alkawarinta. (Tasallah Yuan)