Wamakko Zai Gina Jami’a Mai Zaman Kanta A Sokoto

Shugaban kwamitin tsaro na majalisar dattaban Nijeriya, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko na jam’iyyar APC ya kimtsa domin ginawa da samar da sabon jami’a mai zaman kanta a jihar Sokoto.

Hukumar da ke kula da jami’o’i ta Nijeriya (NUC) ta gabatar wa tsohon gwamnan takardar cike ka’aidar fara neman izinin bude jami’ar wacce za ta kasance mai zaman kanta.

A wata kwafin sanarwar manema labaru da aka rabar wa ‘yan jarida a Abuja, ta shaida cewar an mika takardar cike shirin fara samar da jami’ar wa tsohon gwamnan ne a lokacin da ya kai ziyara ofishin NUC da ke Abuja a ranar Alhamis.

Daga cikin jami’o’i guda 79 masu zaman kansu da su ke Nijeriya, uku kacal daga ciki ne su ke arewa maso yammacin kasar nan wacce ta ke da jihohi bakwai a yankin. Don haka ne a ka yi amannar cewar muddin aka samu wasu karin jami’o’in hakan ai taimaka sosai wajen kyautata ci gaban yanki da ma kasa baki daya.

Wamakko ya ce, burinsa na kafa jami’a mai zaman kanta ya biyo bayan muradinsa na tabbatar da bayar da gudunmawa wajen gina ilimin al’umma mai tasowa nan gaba.

Babban sakataren NUC, Farfesa Rasheed ya jinjina wa yunkurin Wamako na gina sabowar jami’a mai zman kanta.

Ya misalta Wamako a matsayin mai kishin Nijeriya, ya kuma tunatar da yadda dan majalisar ya dafa wa ci gaba sosai wa jami’ar BUK a lokacin da yake matsayin mataimakin shugaban jami’ar, “Za mu bayar da tamu gudunmawar wajen tabbatar da ka cimma muradinka na kafa jami’a mai zaman kanta. Idan aka samu masu irin wannan tunanin mutum 4-5 lallai Nijeriya ta zata ci gaba sosai wajen kyautata shugabanci,” A cewar shi.

Exit mobile version