Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RIGAR 'YANCI

Wasu ’Yan Bindiga Sun Yi Kashe-kashe A Sabbin Hare-haren Kaduna

by Muhammad
February 4, 2021
in RIGAR 'YANCI
2 min read
Fulani
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Rabiu Ali Indabawa,

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari wani yankin Lere da ke Jihar Kaduna a. ‘Yan bindigar sun hari kauyen, tare da bude wuta ba kakkautawa kan wasu mutane. Sun kuma kashe wasu adadin mutane tare da raunata wasu yayin da wasu suka tsere. Wasu ‘yan bindiga guda shida sanye da abin rufe fuska da kuma bakaken kaya sun mamaye Warsa Piti, a Gundumar Mariri da ke Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna suka kashe mutane biyu a jiya, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito. An ce ‘yan bindigar sun yi harbi kakkautawa, inda suka kashe mutanen kauyen biyu kafin su tsere zuwa cikin dajin lokacin da jami’an soji suka isa yankin. Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Mista Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar haka. Ya ce, “Sojoji karkashin inuwar Operation Safe Haben sun ba da rahoton wani hari da ‘yan fashi suka kai a Warsa Piti, a Gundumar Mariri da ke Karamar Hukumar Lere.

“Sojojin da suka samu kiran wayar gaggawa sun tattara zuwa wurin inda suka yi artabu da maharan sannan suka gudu zuwa daji. Duk da haka, an riga an kashe mutum biyu, wadanda aka ambata da suna, Sale Muhammad da Aguno Bawuro. Gwamnati ta ba da rahoton cewa an kai wani harin a Randagi da ke Karamar Hukumar Birnin Gwari yayin da aka kashe wani mutum. “A wani lamarin na daban, sojojin sun kuma bayar da rahoton cewa wasu matasa da ba a san ko su wanene ba sun kai hari a wani matsugunin makiyaya a kauyen Kurmin Bi na Karamar Hukumar Zangon Kataf .

“A cewar rahoton, harin ramuwar gayya ce kawai ga harin da aka kai wa Wawan Rafi. “Makiyayan da ke yankin sun tsere amma maharan sun kashe shanu shida, tare da jikkata wasu hudu. Wani gida ma an kone shi kurmus.” Ya ce gwamna Nasir El-Rufai ya nuna damuwa kan sabbin hare-haren. Ya kara da cewa “ana ci gaba da bincike kan abubuwan da suka faru, yayin da sojoji ke kara sintiri a sassan yankin,” in ji shi.

 

samndaads
SendShareTweetShare
Previous Post

NDLEA Ta Cafke Fasinja Da Hodar Iblis Ta Naira Biliyan Bakwai

Next Post

Makiyaya Daga Kasashen Ketare Ke Kai Hare-hare A Jihata –Gwamnan Ondo

RelatedPosts

Su Sanata Gaya Sun Halarci Sadakar Kwana 40 Na Surukarsa A Ankpa

Su Sanata Gaya Sun Halarci Sadakar Kwana 40 Na Surukarsa A Ankpa

by Sulaiman Ibrahim
2 days ago
0

Daga Ahmed Muh'd Danasabe, Lokoja Ranar Lahadi da ta gabata...

Yadda Zulum Ya Ziyarci Wadanda Harin Boko Haram Ya Rutsa Da Su A Maiduguri 

Yadda Zulum Ya Ziyarci Wadanda Harin Boko Haram Ya Rutsa Da Su A Maiduguri 

by Sulaiman Ibrahim
2 days ago
0

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri Biyo bayan harin da mayakan Boko...

Dalilanmu Na Shirya Aurar Da Zawarawa A Kaduna – Sardaunan Badarawa

Dalilanmu Na Shirya Aurar Da Zawarawa A Kaduna – Sardaunan Badarawa

by Sulaiman Ibrahim
2 days ago
0

Daga Musa Muhammad, Abuja An kammala dukkan shirye-shirye don fara...

Next Post
Ondo

Makiyaya Daga Kasashen Ketare Ke Kai Hare-hare A Jihata –Gwamnan Ondo

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version