Yayin da ake shirye-shiryen dawowa sabuwar kakar wasannin kwallon kafa ta kasar Ingila, kungiyar Wolverhampton Wanderers ta dauki sabon mai horar da tawagar kungiyar bayan ta rabu da Julien Lopetegui.
Sabon kocin, O’Neil ya jagoranci Bournemouth zuwa mataki na 15 a kakar wasan da ta gabata sannan kungiyar ta kawo karshen kwantiraginta da shi a ranar 19 ga watan Yunin 2023.
Gary O’Neil matashi ne mai kwazo kuma mai fasaha, in ji daraktan wasanni na kungiyar Wolves.
Mun yi farin cikin maraba da shi zuwa kungiyar mu, kuma muna fatan cimma nasara tare da shi a Wolves.
Kocin mai shekaru 40 shine koci na hudu da Wolves ta yi cikin shekaru biyu kacal.
Aikinsa na farko a matsayin kocin Wolves zai zo ne ranar Litinin lokacin da Wolves za ta je Old Trafford don karawa da Manchester United.