Connect with us

WASANNI

Wydad Casablanca Ta Kori Mai Koyar Da ‘Yan Wasan Kungiyar

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Wydad Casablanca ta kasar Morocco mai rike da kofin Zakarun nahiyar Afirka ta sallami mai koyar day an wasanta Hussein Amotta, bayan da kungiyar ba ta taka rawar gani a kakar wasa ta bana.

Amotta wanda ya lashe kofin gasar Morocco a  shekara ta 2017, yana daya daga cikin wadanda suka yi takarar gwarzon koci da babu kamarsa a Afirka a 2017 a bikin da akayi a farkon watannan.

Tsohon mai koyar da ‘yan wasan tawagar kasar Masar, Hector Cuper ne ya lashe kyautar da hukumar kwallon kafa ta Afirka, Caf ta gudanar a watan Janairu a Accra, babban birnin kasar Ghana, ciki har da Gernot Rohr mai koyar da ‘yan wasan Super Eagles ta Nigeria.

Wydad ta gabatar da taro a ranar Talata inda ta fitar da sanarwar korar mai koyar da yan wasan  nata tare da mataimakansa, kan kasa taka rawar gani a bana.

Amotta ya karbi aikin horar da Wydad Casablanca a watan Janairun shekarar 2017, inda ya maye gurbin Sebestian Desabre wanda ya koma kungiyar Ismaili ta kasar Tunisia, yanzu kuma shi ne mai koyar da tawagar  yan wasan kasar Uganda.

Wydad mai rike da kofin gasar Morocco mai kungiyoyi 16 tana ta 12 a kan teburi da tazarar maki 13 tsakaninta da Hassania Agadir wadda ke matsayi na daya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: