Da yammacin yau Laraba 25 ga wata ne, shuguban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da gwamnan jihar California ta kasar Amurka, Gavin Newsom, a babban dakin taron al’umma dake birnin Beijing.
Xi ya ce, cimma nasarori wajen raya dangantakar Sin da Amurka tun lokacin da har zuwa yanzu, ba abu mai sauki ba ne, wanda ya cancanci a daraja. Manufofin gwamnatin kasar Sin kan Amurka, har kullum su ne, mutunta juna, da zaman jituwa, da yin hadin-gwiwa bisa cimma moriyar juna. Kasar Sin za ta ci gaba da yin kokari a wannan fanni, kana, tana fatan Amurka za ta bada hadin-kai.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Fashin Daji Da Dama, Sun Kwato Makamai A Sokoto
- Gasar Wasannin Asiya Ajin Masu Bukata Ta Musaman Ta Hangzhou Ta Bayyana Kulawar Da Sin Take Baiwa Wannan Rukuni Na Al’umma
A nasa bangaren, Gavin Newsom ya ce, babu wata dangantakar kasa da kasa a duniya da ta fi dangantakar Amurka da Sin muhimmanci, dangantakar da ta shafi makomar Amurka gami da alfanun al’ummar kasar. Ya yarda da manufofin da shugaba Xi ya bayyana wajen raya dangantakar kasashen biyu, da shaida aniyar kara tuntubar juna tsakanin jiharsa wato California da kasar Sin, da fadada hadin-gwiwarsu a fannonin da suka shafi sauyin yanayi da sabbin makamashi. California din tana son zama kakkarfar abokiyar hadin-gwiwar kasar Sin na dogon lokaci. Bugu da kari, a yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika wasikar taya murnar bikin ba da lambar yabo na kwamitin kula da dangantakar da ke tsakanin kasashen Amurka da Sin na kasar Amurka.
Shugaba Xi Jinping ya yabawa kwamitin bisa kokarin sa kaimi ga inganta mu’amala da hadin gwiwa a tsakanin Amurka da Sin a fannoni daban daban, kana ya taya Henry Alfred Kissinger, murnar samun lambar yabon.
Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, a matsayin manyan kasashe biyu a duniya, yadda Sin da Amurka suke mu’amala da juna ta hanya mai dacewa ko a’a, yana da nasaba da makomar zaman lafiya da bunkasuwa da kuma dan Adam a duniya. Ya ce Sin tana son bin ka’idojin girmama juna, da yin zaman tare cikin lumana, da yin hadin gwiwa don samun moriyar juna, da kara hadin gwiwa tare da kasar Amurka, da daidaita sabanin da ke tsakaninsu, da tinkarar kalubalen duniya tare, don samun moriyar juna, da wadata tare, da kuma amfanawa jama’ar kasashen biyu har ma da duk duniya baki daya.
Shugaba Xi yana fatan kwamitin da kuma abokai daga bangarori daban daban za su ci gaba da nuna goyon baya ga raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka don taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga raya dangantakar kasashen biyu yadda ya kamata.
Kana a wannan rana, shugaban kasar Amurka Joseph Biden shi ma ya mika wasikar taya murnar bikin. (Murtala Zhang, Zainab)