A baya-bayan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da wani muhimmin umarni, dangane da aiwatar da matakan samar da kasar Sin mai zaman lafiya a matakin koli, yana mai cewa, tun bayan taron majalisar kolin JKS na 18, kokarin gina Sin mai zaman lafiya ya cimma manyan nasarori, kana an samar da kyakkyawan yanayi na rayuwar al’umma cikin yanayi na zaman lafiya da wadatar zuci, kuma al’ummar kasar ta sake samun yanayi na daidaito da oda mai karfin gaske.
A lokaci guda kuma, Sin ta zamo daya daga cikin kasashe mafiya tsaro a duniya.Shugaba Xi, ya yi kira da a kara azamar bunkasa matakan samar da Sin mai zaman lafiya bisa matsayin koli, da tabbatar da cewa, an wanzar da ci gaba bisa daidaito a manufar zamanantar da kasar Sin. (Saminu Alhassan)














