Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a karfafa matakan daidaita manufofin ci gaba, tare da aiwatar da shirin hadin gwiwa tsakanin kasarsa da Ecuador, ta yadda za su gina shawarar Ziri Daya da Hanya Daya tare.
Shugaba Xi, ya yi kiran ne a Talatar nan, yayin da yake zantawa da takwaransa na Ecuador Daniel Roy-Gilchrist Noboa Azín a nan birnin Beijing. A cewarsa, kamata ya yi sassan biyu su aiwatar da manufofin hadin gwiwa a fannin makamashi, da albarkatun kasa, da gina ababen more rayuwa, da hada-hadar kudi da sauran fannoni, kana su himmatu wajen lalubo sassan hadin gwiwa a bangarorin tattalin arziki na dijital, da ci gaba marar gurbata yanayi, da sabbin makamashi da fasahar AI.
A nasa tsokacin kuwa, shugaba Noboa, cewa ya yi Ecuador a shirye take ta zurfafa amincewa juna ta fuskar siyasa tare da Sin, kuma za ta ci gaba da tallafawa kokarin Sin na kare ikon mulkin kai da tsaron yankuna, da martaba matsayin Sin dangane da batun yankin Taiwan.
A daya bangaren, Ecuador na dora muhimmancin gaske ga hadin gwiwarta da Sin, ta kuma shirya ingiza hadin gwiwar cimma moriyar juna tare da Sin a fannin cinikayya, da tattalin arziki, da hada-hadar kudi, da hakar ma’adanai, da sabbin makamashi, da kimiyya da fasaha, da raya al’adu da sauran fannoni.
Kazalika, za ta fadada fitar da hajoji zuwa Sin, kuma tana maraba da karin kamfanonin Sin da su zuba jari, da gudanar da harkokinsu a Ecuador, ta yadda hakan zai taimaka wajen bunkasa rayuwar al’umma da cimma burikan raya kasar ta Ecuador. (Saminu Alhassan)














