Matan al’ummar Bin-Per, da ke gundumar Ruff, Kombun a Ƙaramar Hukumar Mangu ta Jihar Filato, sun gudanar da zanga-zangar lumana ranar Talata, domin nuna adawa da kisan mutane 24 da wasu ‘yan bindiga suka yi.
Matan sun yi tattaki a cikin al’ummar garin, suna ɗauke da ganyaye a kawunansu, yayin da suke jimamin waɗanda aka kashe tare da neman gwamnati ta gaggauta ɗaukar matakan kare rayukan mazauna yankin daga sake faruwar irin wannan hare-haren.
Zanga-zangar ta biyo bayan wani hari da aka kai wa al’ummar garin cikin dare, inda wasu ɗauke da makamai suka mamaye gidaje tare da kashe mazauna yankin.
Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar, Mrs Ladi Joshua, ta bayyana cewa matan sun shiga cikin tsananin baƙin ciki sakamakon rasa mazajensu, ‘ya’yansu, ‘yan uwansu da sauran ‘yan al’ummar garin.
Matan sun yi kira da a kawo ƙarshen hare-haren da ake yawan kai wa Bin-Per da sauran al’ummomin Jihar Filato, tare da roƙon hukumomi da su ƙara tsaurara matakan tsaro da kare al’ummomin da ke cikin haɗari.














