Ƴar gwagwarmayar siyasa Aisha Yesufu ta tsoma baki cikin ta ƙaddamar da ke tattare da sakamakon jarrabawar shiga jami’a (UTME) ta 2025, inda ta yi kira da a kori Ministan Ilimi Dr Tunji Alausa.
Shugaban hukumar JAMB Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana cewa matakan hana maguɗi sun haifar da gazawa da yawa, musamman a jihohin Kudu maso Gabas da Legas.
- JAMB: Tangarɗar Na’ura Ne Ya Haifar Da Gagarumar Koma Baya A Sakamakon UTME Na 2025
- ’Yansanda Sun Cafke Mutane 9 Kan Kisan Jigon Jam’iyyar PDP A Adamawa
A martaninta, Yesufu ta yi ikirarin cewa:
“Da Najeriya tana da (tsayayyen) Shugaban ƙasa da tuni ya kori Ministan Ilimi nan take. Wannan mutumin (shugaban Jamb) ya zo ya ce matakan hana zamba ne suka haifar da gazawar da yawa.”
Ta kuma yi tambaya: “Ko an yi wani tanadi domin a yi wa ɗaliban da gazawar da gangan ta shafa?”
Masana ilimi sun lura cewa gazawar ta samo asali ne daga matsalolin tsarin ilimi da koma bayan tattalin arziki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp