Na kan ga hotunan yin amfani da allunan sola da wasu abokanmu ‘yan Nijeriya suka watsa ta shafin Facebook: Wasu na amfani da na’urar a gida don tsimin kudin da ake kashewa. Wasunsu kuma sun bude tashohin cajin waya ta hanyar allunan sola, inda suka kaddamar da sana’ar kai.
Haka zalika, na taba karanta labarai game da yadda ake yawan aiki da allunan sola a kasashen Afirka. Misali, a kasar Zambia, ana gina wasu kauyuka masu fasahohin zamani bisa tushen fasahar allunan sola, inda ake aiki da allunan wajen samar da wutar lantarki, don biyan bukatun hasumiyar samar da sigina ga wayar salula, da makaranta, da karamin asibiti, gami da gidajen mazauna kauyukan, ta yadda aka shigar da manoma, wadanda ba su da damar amfani da wutar lantarki a baya, cikin wata sabuwar rayuwar zamani ta lantarki.
- Sin Na Adawa Da Abubuwan Da Ke Da Alaka Da Ita A Cikin Sanarwar Taron Kolin Washington Na NATO
- Shugaban IOC Ya Jinjinawa Burin Dandalin Wayewar Kan Bil Adam Na Nishan Mai Manufa Irin Ta Olympic
A zahiri, allunan sola sun baiwa mutane damammakin daidaita matsalar karancin wutar lantarki, da kyautata zaman rayuwa a kasashen Afirka. Kana yawancin allunan sola da suke amfani da su, an kera su ne a kasar Sin.
Bisa wata makala da Jaridar SCMP ta yankin Hong Kong na kasar Sin ta wallafa, an ce karfin samar da allunan sola na kamfanonin kasar Sin ya kai kashi 80% na jimillar karfin kamfanonin dake daukacin duniya. Kana yadda kamfanonin Sin ke kokarin rage kudin da ake kashewa domin samar da kaya, da inganta kaya a kai a kai, ya sa allunan sola da suke samarwa zama masu inganci da rahusa. Wannan ma dalili ne da ya sa allunan sola da fitilun sola, da sauran kayayyaki masu aiki da makamashin zafin rana, samun karbuwa a kasashen Afirka.
Sai dai duk wani abu, in dai akwai mai kaunarsa, to ba za a rasa mai kyamarsa ba. A ganin kasashen Turai da kasar Amurka, allunan sola da sauran kayayyakin makamashin sola na kasar Sin sun cika araha, abin da ya sanya allunan sola kirarsu kasa yin takara da na kasar Sin. Saboda haka suna cewa wai kasar Sin na “samar da kayayyaki fiye da kima”, da “ba da tallafi ga kamfanoni” da dai sauransu, har ma a bisa wadannan dalilai sun saka wa kasar Sin takunkumi. Misali, tun daga shekarar 2012, kasar Amurka ta riga ta kaddamar da haraji na hukunci kan allunan sola kirar kasar Sin.
Matakan takunkumi sun haifar da babban matsin lamba kan kamfanonin Sin, amma sun dukufa kan kirkiro sabbin fasahohi, da rage kudin da ake kashewa wajen kera kaya, gami da inganta kaya a kai a kai, ta yadda ake iya samar da kayayyaki masu inganci, da farashi mai rahusa, don biyan bukatun kasuwannin kasashe masu tasowa.
Wannan kokari da kamfanonin Sin suke yi ya sa bukatu kan allunan sola fara habaka tun bayan shekarar 2013, inda yawan allunan sola da aka kafa a kasashe daban daban ya karu da ninki 10 cikin wadannan shekaru da suka gabata. Yayin da kamfanonin kasar Sin masu kera allunan su ma suka samu damar jagorantar tsare-tsaren kera allunan sola na duniya, ta hanyar sabunta fasahohinsu a kai a kai.
A dayan bangaren kuma, kokarin kare sana’ar kera allunan sola da kasashen Turai da kasar Amurka suka yi ya bi ruwa. A kwanan baya, jaridar La Monde ta kasar Faransa, ta watsa wani rahoto game da Dalibor Nikolovski, wani dan kasuwa na kasar Faransa da ya kafa masana’antar kera allunan sola a kasar Sin. A cewar rahoton, tsarin masana’atun samar da kaya mai inganci na kasar Sin, da manufofin kasar na saukaka wa masu zuba jari aiki, da ba su gatanci, sun sa dan kasuwar kaunar kasar Sin, har ma ya dade yana zama a kasar har tsawon shekaru 17. Ko da yake hukumar kasar Faransa ta gayyace shi don ya koma gida ya kafa masana’anta a can, amma dan kasuwar ya ki yarda. A cewarsa, yin haka “ ba zai dace da sanin ya kamata ba”.
Hakika, dangane da allunan sola da sauran kayayyaki masu aiki da makamashi mai tsabta, ko ana samar da su “fiye da kima” ko akasin haka, bai kamata a yanke hukunci bisa matsin lambar da kamfanonin kasashen Turai da na Amurka ke fuskanta ba. Maimakon haka, ya kamata a lura da butakun kasashe masu tasowa, wadanda suke da rinjayen al’ummar duniya. A lokacin da mutane miliyan 600 dake nahiyar Afirka suka kasa samun wutar lantarki, kuma hukumomin nahiyar ke neman habaka tsare-tsaren samar da wutar lantarki ta zafin rana, don sanya karin mutane miliyan 300 na kasashen Afirka samun hidimomi masu alaka da wutar lantarki kafin shekarar 2030, kuma ake daukar matakan takunkumi don hana sana’ar kera allunan sola ta kasar Sin tasowa, a iya cewa wannan mataki bai dace da adalci ba ko kadan. Kana sam ba shi da amfani, wato ko kare kamfanonin cikin gida na kasashen Turai da na Amurka ma ya kasa, balle ma hana ci gaban harkokin kamfanonin Sin, wadanda ke biyan bukatun al’ummar kasashe masu tasowa.
Sai dai mun san su kasashen Turai da na Amurka, sun fara saka harajin kwastam na hukunci kan motoci kirar kasar Sin masu aiki da sabbin makamashi, to ko wane tasiri matakin zai haifar? Sai mu dubi abun da ya faru kan allunan sola domin gano amsar tambayar. (Bello Wang)