ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Aka Taɓa Ɓoye Trump A Motar Kayan Abinci Saboda Tsoron Ka Da Iran Ta Kai Masa Hari

by Sadiq
4 weeks ago

Rahotanni daga kafafen yaɗa labaran Amurka sun ce an ɓoye Shugaban Amurka, Donald Trump, a cikin wata babbar motar ɗaukar abinci a filin jirgin sama domin sauya jirginsa a asirce saboda barazanar da ake zargin Iran na yi masa.

Lamarin ya faru ne a watan da ya gabata, lokacin da Trump ke barin Turkiyya bayan halartar taron ƙungiyar tsaro ta NATO.

ADVERTISEMENT

Rahoton jaridar Washington Post ya ce Trump ya hau jirgin shugaban ƙasa, Air Force One, a bainar jama’a.

Daga nan kuma aka shigar da shi cikin wata motar ɗaukar abinci da ake amfani da ita wajen kai abinci cikin jiragen sama.

LABARAI MASU NASABA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

An yi amfani da motar wajen kai Trump zuwa wani jirgin soji na daban ba tare da ’yan jarida ko wasu ma’aikatan Fadar White House sun san cewa an sauya masa jirgi ba.

Wasu jami’an Amurka sun shaida wa CBS News cewa hukumomin ƙasar sun gano shirin da Iran ke yi na kai hari kan jirgin da Trump ke ciki.

Sai dai Fadar White House ba ta tabbatar da wannan rahoto kai tsaye ba.

Rahotanni sun ce Trump ya isa Turkiyya ne cikin wani sabon jirgi ƙirar Boeing 747-8 da Qatar ta bai wa Amurka, amma lokacin da zai bar ƙasar an tsara zai yi amfani da tsohon Air Force One.

A ranar 8 ga watan Yuli, an ga Trump yana shiga tsohon jirgin Air Force One a filin jirgin Ankara.

Amma a asirce, an kai shi wani jirgin soji ƙirar C-32A ta cikin motar ɗaukar abinci.

Jirgin C-32A wani Boeing 757 ne da ake amfani da shi wajen jigilar mataimakin shugaban Amurka da wasu manyan jami’an gwamnati.

Rahoton ya ce Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, shi ma ya shiga jirgin C-32A ta wata hanya daban domin tabbatar da cewa komai ya tafi yadda aka tsara.

A lokacin da ake gudanar da wannan aikin, ’yan jarida da wasu ma’aikatan Fadar White House sun kasance a cikin tsohon Air Force One.

An kuma ce an umarce su da su rufe tagogin jirgin.

Ba su san cewa Trump ya bar jirgin ba.

Daga nan Trump ya tashi zuwa Birtaniya a cikin jirgin C-32A, inda daga baya ya koma tsohon Air Force One domin ci gaba da tafiya zuwa Amurka.

Trump ya sake hawa sabon jirgin da Qatar ta bai wa Amurka daga Birtaniya zuwa Washington.

A yayin tafiyar, Trump ya yi magana da manema labarai kan barazanar da Iran ke yi masa, amma bai bayyana cewa an sauya jirginsa a asirce ba.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa aka umarci ’yan jarida su rufe tagogin jirgin lokacin da suke barin Turkiyya, Trump ya ce hakan na da nasaba da matsalolin tsaro.

Ya ce yana fuskantar barazana, kuma yana cikin mutanen da Iran ke son ganin bayansu.

“Wataƙila wata rana kana son sauya sana’a,” Trump ya faɗa wa wani ɗan jarida yayin da yake magana kan hatsarin da yake fuskanta.

Daraktan Sadarwar Fadar White House, Steven Cheung, bai tabbatar ko musanta rahotannin cewa an sauya jirgin Trump saboda tsoron Iran ba.

Sai dai ya ce sabon Air Force One jirgin sama ne na zamani wanda aka tanade ɗauke da na’urorin tsaro domin kare shugaban ƙasa da ma’aikatansa.

A baya, hukumomin leƙen asirin Amurka sun yi gargaɗi game da yiwuwar harin da za a iya kai wa Trump ko jiragen da yake amfani da su.

Haka kuma, rahotanni sun ce hukumomin tsaron Amurka sun damu da tsaron sabon jirgin da Qatar ta bai wa ƙasar, musamman saboda ana shirin amfani da shi wajen jigilar shugaban ƙasa.

Amurka ta kwashe watanni tana gyaran wani jirgin Boeing 747-8 da aka ware domin zama sabon Air Force One, wanda ake sa ran gyaran zai ci kusan dala miliyan 400.

Rahotanni sun ce jiragen Air Force One na Amurka suna da wasu na’urorin zamani da za su iya taimakawa wajen kare jirgin daga wasu hare-haren makamai masu linzami.

Sai dai ba a bayyana irin na’urorin tsaron da jirgin da Qatar ta bai wa Amurka yake da su ba.

Fadar White House ta ce sabon jirgin Air Force One yana da cikakkun matakan tsaro da ake buƙata domin tafiye-tafiyen shugaban ƙasa, yayin da ake shirin ƙara wasu na’urorin tsaro a cikinsa.

MASU ALAKA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi
Manyan Labarai

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Next Post
‘Yansanda Sun Ceto Mutane 15 Da Aka Sace Bayan Artabu Da ‘Yan Bindiga A Kogi

'Yansanda Sun Ceto Mutane 15 Da Aka Sace Bayan Artabu Da 'Yan Bindiga A Kogi

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.