Majalisar Dattawa ta yi karatu na farko kan dokar da ta amince da cin tarar Naira 50,000 ga iyayen da suka ki sa ‘ya’yansu su samu ilimin makarantun Firamare da Sakandare,dokar da Sanatato Orji Kalu ya bukaci ayi mata gyara a sashi na (4) sakin layi na (b) na dokar inda aka goge Naira 2,000 inda aka maida Naira 20,000; sashe na (4) sakin layi na(c) inda aka sa Naira 5,000 aka sauya ta Naira 50,000 yayin da sashi na 3 sakin layi na (2) an sa dokar Naira 10,000 amma sai aka maida ta zuwa Naira 100,000.
Da yasa albarkacin bakin shi tsohon Shugaban majalisar dattawa ta kasa a majalisa ta tara Sanata Ahmed Lawan ya ce idan aka maida hankali akan ilmin ‘ya mace hakan zai bunkasa cigaban kasa sosai.
Lawan ya bayyana hakan ne ranar Laraba a wani bayani da mai ba shi shawara na harkokin yada labarai Ezrel Tabiowo ya raba wa manema labarai, saboda bikin ranar ilimin ‘ya mace na kasa da kasa.
- Kashun Da Nijeriya Ke Fitarwa Ya Karu Daga Naira Biliyan 116 Zuwa 146.1
- Za A Binciki Yadda Aka Karkatar Da Tallafin Korona Naira Biliyan 183.9
Kamar yadda ya ce, dan majalisar da yake wakiltar mazabar majalisar dattawa ta Yobe ta Arewa a majalisar dattawa ya kara jaddada cewa ilmantar da ‘ya mace samar da wata dama ce gare ta, ta yadda bada tata gudunmawar cigaban al’umma.
Shi ma Babban lauya na kasa Femi Falana cewa ya yi abu mafi dacewa shi ne majalisun kasar su tabbatar da yin dokar tsarin mulki da hakan zai ba Akanta Janar na kasa a kan ya cire daga asusun Jihohin zuwa gidauniyar kula da al’amuran ilimi.
Ga dai mganar da ya yi: “A tsarin da aka yi a na tunawa da ranar ‘ya mace ta kasa da kasa ta 2023 wadda aka yi ranar Alhamis, ‘yan majalisar wakilai ta kasa ba tare da wani bata lokaci ba suka amince da kudurin da suka cimmawa na sa ma’aikatar ilimi ta tarayya ta rage yawan yara ‘yan mata da basu zuwa makaranta, ta hanyar tabbatar da samar da ilimi kyauta kuma dole na ‘ya’ya mata a fadin tarayyar Nijeriya.
Ita ma ‘yar majalisar wakilai ta kasa Kafilat Ogbara (APC-Legas) da tace gidauniyar kasa da kasa kan al’amuran gaggawa na yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF ta bayyana cewa akwai yara milyan 18.5 da basu zuwa makaranta inda kashi 60 ya nuna yara mata ne.Ta jaddada ‘yanmata suna da dama ta kasancewa ba wani abinda zai dame su,na da ilimi, da rayuwa mai cike da lafiya.
Honorabul Ogbara ta bayyana idan aka kul da rayuwar ‘yan mata sosai,ya kunshi samar da wani babin da zai ba ‘yanmata dama su rika bada gudunmawar su kan kowane tsarin da aka dauka.