ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, July 27, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Ake Hada Sabulun Wanki Na Sayarwa

by Bilkisu Tijjani
3 years ago
Sabulun Wanki

Jama’a barkammu da warhaka. Yau za mu yi duba akan yadda ake hada sabulun wanki. Sabulun wanki shi ne sabulun da ake amfani da Shi wajen wanke tufafi domin cire dauda da warin da yake a jikin tufafi.

Yana da kyau sabulun wanki ya zama ingantacce domin cire daudar da ke jikin kayan.wajen hadin sabulu, a tabbata an yi amfani da turaren hadin sabulu mai kamshi don Jan hankalin masu saya, turare mai dadi sirri ne sosai wajen daukar hankali.

  • Sin Na Fatan Amurka Za Ta Yi Gamsasshen Bayani Game Da “Nord Stream”
  • Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Matsayinta Na Warware Matsalar Ukraine A Siyasance

Sinadaran da ake hadawa da su su ne:

ADVERTISEMENT

Da farko Yana da kyau mai son ya hada sinadaran da ake hada sabulu ya tanadi; 1. Costic Soda, 2. Soda Ash, 3. Sulphat, 4. Silkate, 5. Kwakwa. 6. Kala (ta ruwa GA masu bukata) 7. Gwangwani, 8. Roba ko mazubi, 9. Ma’auni (misali Kofi ko gwangwani), 10. Safar hannu

Matakan da Ake bi wajen tsuma sinadaran sabulu su ne:

LABARAI MASU NASABA

Aure Ba Ya Ruƙuwa Sai Da Sana’a

Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC

Da farko dai za ka samu ‘yan robin ka guda uku lafiyayyu ba dole sai roba ba mazubinka guda uku, bayan ka same su sai ka samo ruwa shi ma ka aje a kusa da kuma abin da za ka yi amfani da shi a matsayin ma’auni kar ka canja shi har mun gama, misali kofi ko wani ko idan ka tanaji wadannan abubuwan.

Sai kuma mataki na farko: Zuba ma’auninka uku na ruwa a cikin roba ko mazubi na daban, sai ka debo costic soda shi ma ma’auni uku ka zuba a cikin ruwan da ka zuba a robar.

Mataki na biyu: Debo ruwa kashi daya bisa hudu (1/4) na ma’aunin da ka yi amfani da shi na costic soda ka zuba a cikin wata robar har ila yau ita ma Soda Ash ka debo kashi daya bisa hudu ka zuba a cikin ruwan, ita ma sulphat ka yi mata irin na Soda Ash.

Bayan ka yi haka sai ka zuba su a wurin da ka hada Costic Soda dinka.ka dauko silket shima daya bisa hudu (1/4) na ma’auninka ka sa cikin hadin.

Daga nan kuma sai ka dauko man kwakwarka ka sa ma’auni biyu a cikin kwabin da ka yi, ka zuba kala ta ruwa in kana son kamshi to sai ka ci gaba da motsawa, za ka ga ruwan yana dunkulewa ka ga ya dunkule wato Sinadaran sun hade sosai sai ka samu gwangwaninka ka rika zuba hadin ka ajiye shi har ya bushe to in sha Allah za ka ga sabulunka ya hadu lafiya lau in ka sa kala za ka gan shi ya yi taurinsai ka sayar.

Kana iya samun kayayyakin a wurare daban-daban kamar kasuwa, kamfanoni da online wato kayan hadin.

Allah ya ba da sa’a.

Sabulun Wanki
Bilkisu Tijjani
+ postsBio
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Faten Dankalin Turawa Da Kaza
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Muhimmancin Kula Da Gashi Domin Lafiyarsa Da Kyawunsa
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Abubuwa Shida Da Ya Kamata Mace Ta Sani Kafin Ta Yi Aure
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Miyar Karkashi Da Nama

MASU ALAKA

Aure Ba Ya Ruƙuwa Sai Da Sana’a
Labarai

Aure Ba Ya Ruƙuwa Sai Da Sana’a

January 24, 2026
Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC
Sana'a Sa'a

Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC

August 3, 2025
Sana’ar Hada Sabulun Aloe Vera
Sana'a Sa'a

Sana’ar Hada Sabulun Aloe Vera

February 1, 2025
Next Post
Wakilai 2977 Na Npc Karo Na 14 Suna Wakiltar Moriyar Yawancin Sinawa

Wakilai 2977 Na Npc Karo Na 14 Suna Wakiltar Moriyar Yawancin Sinawa

LABARAI MASU NASABA

Auto Draft

ADC Ta Buƙaci Tinubu Ya Bai Wa Waɗanda Aka Sace A Kaiama Da Borno Kulawa

July 27, 2026
Sabulun Wanki

Sojojin Ruwa Sun Cafke Jirgin Ruwa Maƙare Da Ɗanyen Mai Na Sata

July 26, 2026
Sin Za Ta Ci Gaba Da Kare Ikon Mulkin Yankuna Da Hakkoki Da Moriyarta Ta Teku

Sin Za Ta Ci Gaba Da Kare Ikon Mulkin Yankuna Da Hakkoki Da Moriyarta Ta Teku

July 26, 2026
Xi Jinping Ya Mika Sakon Murnar Cika Shekaru 61 Da Samun ‘Yancin Kai Ga Shugaban Maldives

Xi Jinping Ya Mika Sakon Murnar Cika Shekaru 61 Da Samun ‘Yancin Kai Ga Shugaban Maldives

July 26, 2026
Sabulun Wanki

Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Naɗa Sabon Mai Ba Shi Shawara

July 26, 2026
Sin Ta Ayyana Shirin Ko-ta-kwana Na Samar Da Tallafin Gaggawa Ga Lardin Guangdong

Sin Ta Ayyana Shirin Ko-ta-kwana Na Samar Da Tallafin Gaggawa Ga Lardin Guangdong

July 26, 2026
Fina-finan Kasar Sin Suna Haskakawa Tare Da Samar Da Dimbin Kudaden Shiga A Zangon Nuna Fina-finai Na Lokacin Zafi Na Bana

Fina-finan Kasar Sin Suna Haskakawa Tare Da Samar Da Dimbin Kudaden Shiga A Zangon Nuna Fina-finai Na Lokacin Zafi Na Bana

July 26, 2026
Shugaban Senegal Ya Jinjinawa Kasar Sin Bisa Taimakon Gina Zaurukan Gudanar Da Wasannin Gasar Olympics Ta Matasa

Shugaban Senegal Ya Jinjinawa Kasar Sin Bisa Taimakon Gina Zaurukan Gudanar Da Wasannin Gasar Olympics Ta Matasa

July 26, 2026
Sabulun Wanki

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Alƙalin Babbar Kotu A Kebbi

July 26, 2026
Bala Mohammed

Sadakin Budurwa ₦3,000 Na Bazawara ₦1,500: Gwamnatin Bauchi Ta Ƙaryata Batun

July 26, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.