Kamfanin Nestlé Milo ya tallafa wa masu sana’ar sayar da shayi 2,000 a Kano da Jos ƙarƙashin shirinsa na tallafa wa kwastomomin da suka jima suna hulda da shi domin ƙarfafa gwiwar masu kananan sana’o’i.
Kamfanin ya ce rabon tallafin zai kuma ƙarfafa rawar da Milo ta shafe tsawon shekaru tana takawa a matsayin mahadin shan shayi a Arewacin Nijeriya.
Shirin ya bai wa masu shayi kayan tallafin da suka hada da risho mai amfani da iskar gas, tukunyar gas, malafar kare rana, fitila mai amfani da hasken rana, kofuna da kuma sinadarin Milo.
Masu shirya taron sun ce an kaddamar da shirin ne domin karrama rawar da masu shayi ke takawa wajen samar da karin kumallo a kullum a Arewacin Nijeriya, tare da taimaka musu wajen bunƙasa sana’o’insu.
Da yake jawabi a yayin taron da aka gudanar a Kano a makon da ya gabata, wakilin kamfanin na Nestle Milo a Nijeriya, Gilbert Tweneboah-Koduah, ya ce wannan tallafi na nuna yadda kamfanin ke son inganta alaka da al’umma.
Ya kuma ce shirin ya fara ne bara da masu shayi 400, amma yanzu an faɗaɗa shi zuwa mutum 2,000 a biranen Kano, Jos, Kaduna da Maiduguri, tare da shirin ƙara faɗaɗa shi zuwa fadin Arewacin Nijeriya.
Shugaban Ƙungiyar Masu Sayar da Shayi ta Jihar Kano, Usman Muhammad Usman, ya yaba wa Nestlé Milo bisa goyon bayan da ya daɗe yana ba su tsawon lokaci.














