ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Aure Ba Ya Ruƙuwa Sai Da Sana’a

by Ibrahim Bala
8 months ago
Aure

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu.

Jama’a barkanmu da kasancewa tare da wannan fili mai albarka, filin da ya saba zaƙulo muku batutuwan da suke ci wa al’umma tuwo a kwarya.

Kamar kowane mako a yau ina so nayi magana akan iyaye da samari, sannan kuma zan yi magana akan aure gabaɗayansa.

ADVERTISEMENT

A ‘yan lokutan nan ko na ce a ‘yan shekarun nan, za a ga yara ne ƙanana suke ta yin aure, magana ta gaskiya aure ba magana ce ta wasa ba. Ya kamata a riƙa lura, shi ya sa za a ga zawarawa yara ƙanana suna da yawa, ba don komai ba sai don akwai wasu abubuwa da ba ma iya kulawa a auren.

  • Ɓata-gari Sun Kashe Matar Aure Da ’Ya’yanta 3 A Kano
  • Yadda Takaddama Ta Kaure Bayan Ceto Daliban Neja 130

Na farko iyaye wasu kawai sun damu ‘yarsu ta yi aure, ko kuma yaron yana yawan kashe mata kuɗi, ko yayi lefe masu kyau, ko ya biya kuɗin na gani ina so da kyau, ko dan gidan su wasu ne. Na biyu kuma, yaran auren a baki kawai suke jin shi, ‘yar budurwa ta ɗan yi kyau, ta ɗan fara shekaru, fara ce sai na aure ta. 

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Su kuma iyaye wani lokacin yana ɗan yin sana’arsa, magana ta gaskiya kuma, ba ma son mu vata masa rai, idan ba a yi masa aure ba. Duk waɗan nan abubuwan ba su ne abun lurar ba, dole aure baya ruƙuwa sai da sana’a, sana’ar ma mai ƙwari wacce ba wai kai kaɗai za ka ci da kanka ba, shin za ka iya riƙe wani? shi ne abun lura.

Idan aiki kake yi, aikin da kake yi albashin zai iya isar ka bayan ka ciyar da matarka har a samu ɗan wani abun?. Saboda mu’malata rayuwa, kuɗin haya, rashin lafiya ko wata irin larura, dole sai muna iya kallon abun.

Magana ta gaskiya aure ba zai ruƙu ba sai da sana’a, duk gatanka ba zai ruƙu ba sai da sana’a. Aure wani lokacin tamkar doguwar mota ce dole kullum za ka sha mai. Ko kai kanka kasan da wahala ba a ɗan tsaya a gareji ba, ko kuma wani abun.

To, aure na buƙatar kulawa, ba zai ruƙu ba sai da kuɗi, kuma kuɗi ba zai ruƙu ba sai da sana’a. Duk mtumin da za a ce kullum zai ɗauko zai baka sai ya gaji, amma aka ce kai kake da hanyar samu da za ka riƙe gidanka to, sai ka yi wannan. Shi hankali ba a yarinta yake ba, daman duk mutumin da zai mayar da hankali akan sana’a to, yana da hankali kenan.

Ba maganar a yi sauri bane, ko shi yaro ya matsa yana son iyali duk ba wannan abun bane ba. Duk mijin da ka gani a duniya akwai matarsa, duk matar da ka gani akwai mijinta. Sai mun tsaya mun nutsu ba don komai ba, sai don yanayi na rayuwa, zawarawa sun yi yawa.

Sannan za ka ga wani yaron ɗan ƙanƙani ‘yar sana’ar sana’ar da yake yi ma daƙyar ake ci da matar, amma ya zo ƙara neman aure. Dan Allah mu nutsu duk mu kiyaye dokokin Allah, ba kai za ka aurar da ita ba, ikon Allah ne da yardar sa.

Amma mu kawai da an zo neman aure, an kawo kuɗi, za a yi caraf a karve, babu bincike, wani ma ƙarya yake yi. Idan ka buncike shi ma, sana’ar ta ƙarya ce.

Allah ya sa mu dace, Allah ubangiji ya zaunar da yaranmu, ƙannenmu da matanmu lafiya. Amin. 

Wassalamu Alaikum

Aure
Ibrahim Bala
+ postsBio
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Matsalar Ƙwacen Waya: Ina Mafita?
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Falalar Goman Farko Na Zul-hajji 

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Sin Za Ta Ci Gaba Da Taka Muhimmiyar Rawa A Ayyukan Hukumar IMO

Sin Za Ta Ci Gaba Da Taka Muhimmiyar Rawa A Ayyukan Hukumar IMO

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.