ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Ake Miyar Margi Da Kifin Tarwad

by Bilkisu Tijjani
3 months ago
Margi

Miyar Margi na daga cikin shahararrun nau’ikan abin ci da ake yi a yankin Adamawa musamman wajen Yola. Wannan miya tana da dandano na musamman saboda amfani da kifin tarwada da kayan kamshi masu kara armashi.

Abubuwan da ake bukata:

Kifin Tarwada mai kyau, Ganyen Yakuwa ko kubewa, Albasa,

ADVERTISEMENT

Attarugu da Tattasai, Kayan yaji, Gishiri, Magi, Man gyada kadan,

Kuli-kuli dan kadan, Garin Gero ko Masara domin kauri.

LABARAI MASU NASABA

Tuwon Alkama Da Miyar Taushe

Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna

Yadda Ake hadawa:

Da farko za a gyara Kifi Tarwada sannan a wanke shi da ruwa mai tsafta. Bayan haka a zuba shi cikin Tukunya tare da albasa, gishiri da kayan yaji domin ya dan tafasa.

A gefe guda kuma, a daka tattasai, attarugu da albasa tare. Bayan kifin ya kusa dahuwa, sai a zuba wannan malkadadden kayan miya cikin Tukunya.

Daga nan sai a saka ganyen yakuwa ko kubewa bayan an wanke su sosai. A rage mata wuta, a bar miyar ta dan dahu a hankali domin kayan hadin su hadu da kyau.

Ana iya zuba dan man gyada kadan domin kara dandano da kamshi. Wasu kuma kan saka Kuli-kuli domin ya kara armashi ga miyar.

A karshe sai a dan zuba garin gero ko masara da aka gauraya da ruwan domi, domin  miyar ta yi kauri yadda ake so. A bar ta ta tafasa na ‘yan mintuna kafin a sauke.

Yadda Ake Ci:

Miyar Margi ta ’yan Yola tana da dadi sosai idan an ci ta da tuwon masara ko tuwon gero. Wannan miya tana daga cikin abin cin gargajiya da ke nuna al’adun mutanen Adamawa da kuma kwayukan su wajen sarrafa abin ci mai armashi.

Margi
Bilkisu Tijjani
+ postsBio
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Tuwon Alkama Da Miyar Taushe
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa

MASU ALAKA

Tuwon Alkama Da Miyar Taushe
Girke-Girke

Tuwon Alkama Da Miyar Taushe

September 5, 2026
Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
Girke-Girke

Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna

August 29, 2026
Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice
Girke-Girke

Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice

August 29, 2026
Next Post
Darajar Naira Ta Sauka A Kasuwar Musayar Kuɗaɗe

Darajar Naira Ta Sauka A Kasuwar Musayar Kuɗaɗe

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.