ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Ake Wainar Masara Da Miyar Yaji

by Bilkisu Tijjani
3 months ago
Masara

Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa daku a Wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata

A yau shafin na mu zai koya mana yadda ake Wainar Masara da Miyar Yaji:

Wainar masara na daga cikin abincin gargajiya da Hausawa ke matukar so. Ana iya ci da safe ko yamma tare da miya mai dandano.

ADVERTISEMENT

Yadda ake hadawa:

Kayan hadin Wainar Masara:

LABARAI MASU NASABA

Tuwon Alkama Da Miyar Taushe

Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna

Masara (ko garin masara), Albasa, Yis, Gishiri kadan, Ruwa, Man gyada.

Yadda Ake hadawa:

Da farko a jika masara na tsawon sa’o’i shida zuwa takwas. Bayan ta yi laushi, a wanke ta sannan a kai nika tare da albasa.

A zuba gishiri kadan a cikin nikakken kullin tare da yis karamin cokali, sannan a gauraya sosai. Sannan a rufe a ajiye a wuri mai dumin abarshi na tsawon Awa daya.

A dora kaskon waina a wuta, a shafa masa mai kadan. Sai a dinga zuba kullin a hankali cikin ramukan kaskon, a rufe har ya soyu.

Bayan ya yi launin zinariya, a juya dayan gefen domin ya gama gasuwa. Daga nan sai a sauke.

Kayan Hadin Miyar Yaji:

Tattasai, Attarugu, Albasa, Kayan kamshi ( Kori, Tayim da sauransu), Magi, Gishiri, Man gyada, Nama ko kifi (idan ana so)

Yadda ake hada Miyar Yaji:

A markada tattasai, attarugu da albasa tare.

A dora tukunya a wuta, a zuba mai kadan sannan a soya albasa.      Bayan haka a zuba markadadden kayan miya.

A bar su su dahu sosai sannan a saka kayan kamshi, gishiri da magi.

Idan ana amfani da nama ko kifi, a saka a wannan lokaci. A ci gaba da dafawa har sai miya ta yi kauri kuma ta hadu da kyau.

Yadda Ake ci:

A jera wainar masara a faranti sannan a zuba miyar yaji a gefe ko a sama gwargwadon yadda ake so.

Wannan abinci yana da dandano sosai, kuma ya dace a ci shi da shayi ko abin sha mai sanyi.

Allah Ya sa a gwada lafiya.

Masara
Bilkisu Tijjani
+ postsBio
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Tuwon Alkama Da Miyar Taushe
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa

MASU ALAKA

Tuwon Alkama Da Miyar Taushe
Girke-Girke

Tuwon Alkama Da Miyar Taushe

September 5, 2026
Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
Girke-Girke

Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna

August 29, 2026
Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice
Girke-Girke

Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice

August 29, 2026
Next Post
Gwamnati Ba Za Ta Saki ’Yan Ta’adda Ba Duk Da Kisan Tsohon Kakakin DHQ — Tinubu

Gwamnati Ba Za Ta Saki ’Yan Ta’adda Ba Duk Da Kisan Tsohon Kakakin DHQ — Tinubu

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.