Idris Aliyu Daudawa" />

Yadda Gawayi Ya Ke Ga Lafiyar Dan Adam

Gawayi shima yana daya daga cikin aya  abubuwan da mutane ke dauuka kamar wani abin banza a gida. Ana dauka shi da muhimmaci ne kawai lokacin da bukatarsa ta taso. Amma kuma, matukar ana neman taimako na farko (first aid) shi gawayi  wani abu ne da ya kamata a bukata a kowanne lokaci. Ba za ka fahinci wannan ba, amma dai dai yana daga cikin magunguna da ya kamata ka tanadar a gida saboda gudummawa da yake bayarwa. Wata kila, ba ka ba shi daraja ko muhimmanci. To lokaci ya yi da ka dauke shi da muhimmanci. Ga dai jerin amfanin gawayi guda goma sha uku da ba ka tsammani kamar haka:

Ya na cire wari:

Idan takalman mutum  da wari;  ka samu gawayi ka sanya ciki, ko kuma idan a cikin daki ne sai ka nemi wurin da yake  ka jefa gawayi zai daina warin ne kawai, ko kuma idan firinji (fridge) ne cikin ke da wari sai a jefa gawayi ciki zai daina. Saboda haka gawayi na dauke wari ko wanne iri ne in ya dame ka

Ya na kashe gubar da ke cikin abincin (kayan lambu):

Al’umma kan koka kan yadda ake amfani da takin zamani ga kayayyakin abincin da muke nomawa musamman ma kayan lambu wadanda sakamakon sa takin kan kasance kamar da guba a cikinsu. To kawai in ka samu irin wadannan kayayakin lambun sa gawayi ciki ka barshi zuwa safiya.

Yana taimaka wa abinci mai rubewa (kayan lambu) ya jima bai lalace ba.

Ya na gyara hakora su yi haske:

Idan  kuma mutum na son hakorin shi ya yi haske, kar ya wani bata  lokacin shi wajen sauraron abin da masu tallar kayayyakin wanke hakori su ke cewa, kawai samu gawayinka ka nika ya yi laushi. Sai ka sami hancin plantain (ayaba) ka rika tsomawa kana goge hakoran na tsawon mako daya.

Ya na sake gyaran miyar da ta yi shirin lalacewa:

Idan miya tana niyar lalacewa in ta kwana da safiya kawai kar ka zubar nemi gawayi ga jefa cikin miyar a kora kan wuta a dumama ta, ita miyar zata dawo darajar ta kamar yadda aka santabda farko.

Ya na rage karfin abin sha mai alamar bugarwa:

Duk abin sha mai dauke da gas idan ya kwana, in kana shakkar sha don wani abu da ka ji. Kawai tauna gawayi ka sa a ciki ka sha, an wuce wurin kenan.

Ya na cire tsami a cikin kunun zaki:

Idan baka son kunun zakin da aka dama ya yi tsami kamar giya, ta zarar an dama kunun sai a nemi gawayi a jefa ciki ya kwana zuwa safiya, lafiya lau zai kasance.

Ya na gyara fuskar da kuraje suka bata:

Kawai sai a samu damar nika gawayi a shafa a wurin.

Ya na busar da gyambo mai mugunya in aka kaka aka kuma sa garin a ciki.

Yana taimakawa wajen kwantar da dattin cikin ruwa in aka jefa shi a  ciki.

Idan cikin mutum ya kumbura a shafa gawayi a kai zai sace cikin lokaci kalilan.

Yana cire dattin da ya kama jikin tiles a bayan gida ko dakin girki (kichen).

Yana kuma maganin gyambon ciki (Ulcer) kasance mai taunawa akai-akai zai taimaka matuka sosai.

Exit mobile version