Sister Iyami Jalo Turaki 08064666847 sisteriyami@gmail.com|
Assalamu alaikum, barkanmu da warhaka, sannunmu da arzikin sake haduwa a wannan fili namu mai albarka raino da tarbiyya.
Yau filin zai yi tsokaci ne kan iyaye kansu. Mafi akasari iyaye a yanzu ba’a ba wa yara kulawar da ta dace, uwa tana tare da waya tana hira “Chatting,” uba yana tare da waya yana chatting, an kyale yara karkashin talabijin su kalli tashar da ta dace har su kalli abin da bai dace ba, ku iyaye kuna can kuna chatting sai abubuwa sun kwabe a zo ana kuka da cewar ba irin tarbiyyar da ban ba wa Iyaye maza da mata ya kamata mu rage ba wa waya muhimmanci, farko mu lura da yaya rayuwar ‘ya’yanmu take tafiya, idan uwa ce tana chatting har abinci ya kone, in uba ne har a idar da Sallar jam’i yana chatting.
Yana da kyau mu tsara komai yadda zai tafi daidai a kan tsari ta yadda ba za’a samu matsala ba. ‘Ya’yanmu su ne komai namu mu yi kokarin ganin mun inganta tarbiyyarsu ta yadda a gabanin tsufanmu za su ji tausayinmu su yi mana abin da ya dace na karashen rayuwarmu.
Yana da kyau a lokacin da suke gida mu ba su dukkanin lokacinmu domin shi suka fi bukata. Idan sun tafi makaranta sai mu koma ga wayoyinmu. Wata uwa har yara su dawo daga makaranta ba ta gyara gida ba balle ta dora abinci, wanda hakan ba daidai bane.
Wani uban kuma yara ba su isa su zo inda yake ba idan ya dawo gida, yin hakan yana rage kauna da shakuwa a tsakani, yadda aka tarbiyyantar da su tun suna kanana haka za su tashi da shi har girmansu. Mu rage ba ta lokacinmu a kan waya, mu mayar da hankali a kan raino, kula da tarbiyyar yaranmu a daidai wannan lokaci da zamani ya sauya komai. Allah ya sa mu gyara.