An bayyana cewa, moman rani ya taimaka matuka wajen rage kwarara mutanen kauyawa zuwa birane, musamman domin zuwa ci-rani.
Alhaji Shu’aibu Bawa, Shugaban Karamar Hukumar Kudan da ke a Jihar Kaduna ne ya sanar da hakan, inda ya kara da cewa, rungumar aikin noman rani da al’umma mazauna yankin musamman matasa suka yi, hakan ya rage yawan adadin masu zuwa birane domin domin yin sana’o’in rani.
A cewarsa, sama da manoma dubu uku ne ke ci gaba da amfana da madatsar ruwan da ke yankin, bayan an yashe shi na zurfin mita biyar, shekara 40 bayan an haka shi domin noman rani.
Shugaban ya ci gaba da cewa, a don haka ne hukumar ta yanke shawarar gina wa jama’ar da ke yankin kasuwar zamani don a kara habaka hada-hadar kasuwancin amfanin gona a yankin da kuma a fadin jihar kaduna.
Alhaji Shu’aibu ya bayyana cewa, yankin na a kan gaba wajen noman rake a Jihar, amma kasancewar Makarfi cibiyar kasuwancinsa ya sa Makarfin ta fi ta shahara a harkar raken.
A cewar shugaban, manoma a yankin na noma sama da kashi 65 na kayan marmari na noman rani da ake samarwa a Jihar Kaduna, inda ya kara da cewa, yankin na a kan gaba da babbar kasuwar Mile 12 da ke a jihar Legas wacce ta shahara wajen kasuwancin kayan gwari.