Yadda Tambuwal Ya Inganta Ayyukan Hukumar Kashe Gobara A Sakkwato

Duk da muhimmanci da tasirin da ke ga Hukumar Kashe Gobara a rayuwar al’umma amma Jihohi 15 ne kacal suke ta Tashoshin Kashe Gobara a kasar nan wanda hakan yake matsayin babban kalubale da hadari ga al’umma da dukiyoyinsu.

A watannin da suka gabata kafafen yada labarai sun ruwaito Kunturola – Janar na Hukumar Kashe Gobara ta Kasa , Joseph Anebi yana bayyana cewar sun damu kwarai da rashin ingantattun tashoshin kashe wuta a wasu jihohin domin a cewarsa Jihohi da dama ba su da Hukumar Kashe Gobara wadda ke aiki yadda ya kamata.

Shugaban Hukumar ta Kasa ya bayyana hakan ne a yayin da manbobin Kwamitin Ayyukan Cikin Gida na Majalisar Wakilai suka ziyarci Hedikwatar Hukumar a Abuja tare da kira ga Majalisa da ta hanzarta wajen gyaran fuska ga Kundin Dokar Kashe Wuta ta 1963 domin karfafa kafa Cibiyoyin Kashe Wuta a fadin kasa bakidaya.

Shakka babu ruwa da wuta a cikin tsarin rayuwar al’umma suna matsayin sinadarin maslaha ko akasinta. Hasalima yawaitar ko rashin daya daga cikinsu a kan iya canza matsuguni, masalaha a kai, annobar barnar ruwa a karshe ta kan iya zama gyara, sabanin annobar bala’in gobara wadda jaje, neman taimako, da addu’o’i kan biyo baya.  A bisa ga gani ko jin tarihin yadda bala’in annobar wuta ke salwantar da rayuka da dukiyoyin al’umma, shigarsa ofis zuwa yau, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi hobbasar kwazon inganta Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Sakkwato.

A bayyane yake cewar a Jihar Sakkwato wadda Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ke shugabanta a kasa da shekaru uku ba wai kawai akwai ingantacciyar Hukumar Kashe Gobara kawai ba a’a , akwai kuma wadatattun kayan aiki da kwararrun ma’aikata wadanda ke zaune a shirin ko-ta-kwana domin kai daukin gaggawa idan bukatar hakan ta kama.

A yau Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Sakkwato ta samu nasarori da ci-gaba daban-daban wadanda al’ummar jihar ke yabawa kan muhimmancin da Gwamnatin Jiha ta baiwa fannin wanda a wasu jihohin aka samu akasin hakan .

A kokarin ganin ayyukan Hukumar sun rika tafiya yadda ya kamata Gwamnatin Tambuwal ta siyo sababbin motocin kashe gobara na zamani guda 10 tare da gyara tsofaffinmotoci n da Hukumar ta ke da su wanda hakan ya kawo adadin motoci 18 da Hukumar bakidaya take da su .

Ba sai an fada ba samar da wadattaun ruwa abu ne mai matukar mihimmanci ga ayyukan Hukumar Kashe Gobara a ko’ina a duniya domin idan har babu wadatattun ruwa to a kan samu tangarda sosai, domin kamar yadda aka sani baya ga motocin aiki ruwa su ne kashin bayan tafiyar da ayyukan Hukumar. A kan wannan Gwamnatin Jiha ta yi hobbasar kwazon gina rijiyoyin bohol guda biyu wato daya a Hedikwatar Hukumar a Arkilla da kuma daya a ofishin Hukumar da ke a kan titin Sarkin Musulmi Abubakar tare kuma da samar da manyan motoci biyu masu daukar litar ruwa dubu 30, 000 wadanda ke biye da motocin kashe wuta a cikin shirin ko-ta-kwana.

A bisa ga fadadar Birnin Sakkwato da karuwar yawan al’umma a yanzu haka Gwamnatin Jiha ta sha alwashin gina sababin tashoshin kashe wuta guda takwas wadanda za a samar a Tsohuwar Kasuwa da Sabuwar Kasuwa domin kare afkuwar gobara a kasuwannin wadanda a lokutan baya ‘yan kasuwar suka tafka asarar dimbin dukiya. Sauran sababbin tashoshin za a yi su ne a unguwannin Bado, Kalambaina, More, Mana, Mabera da titin Sama duka a cikin kwaryar Birnin Sakkwato.

Haka ma a kokarinta na ganin ta kara bunkasa ayyukan Hukumar Kashe Gobara tare da baiwa daukacin al’ummar Jihar Sakkwato kariyar da ta kamata, a yanzu haka Gwamnatin Tambuwal ta bayar da himma wajen samar da Tashoshin Kashe Goabara a Yankunan Majalisar Dattawa uku a Yammaci, Kudanci da Arewacin Sakkwato wato a Kananan Hukumomin Wurno, Gwadabawa, Tambuwal da Tangaza domin bayar da agajin gagawa idan bukatar hakan ta kama a wadannan yankunan.

Baya ga wannan Hukumar ta kan wayar da kan al’umma kan hadari da illar gobara tare da bayyana matakan da za a iya dauka domin kaucewa fadawa cikin mummunan hadarin gobara. Ire-iren wadannan fadakarwar Hukumar kan yi su ne a kafafen yada labarai na Radiyo da Talbijin duka dai domin ganin sun sauke hakkin da ya rataya a wuyansu na ilmantar da jama’a hadarin gobara da muhimmancin daukar matakin gaggawa domin kaucewa faruwar hakan a yau da gobe.

Shin ko Hukumar Kashe Goabara a Sakkwato ta na daukar matakin gaggawa a yayin da gobara ta tashi a gidajen al’umma? Ita ce tambayar da wakilin mu yayi wa Shugaban Hukumar Kashe Goabara ta Jihar Sakkwato, Alhaji Murtala Mohammed wanda ya amsa da cewar “Muna kai daukin gaggawa a duk lokacin da muka samu rahoton tashin wuta ba tare da bata lokaci ba domin ma’aikatan mu suna zaune a cikin shirin ko-ta-kwana. Baya ga motocin kashe wuta, muna kuma tafiya tare da manyan motoci (tirela) da ke dauke da ruwa domin ganin dai an samu shawo kan wuta cikin hanzari.”

Shugaban Hukumar ya kuma bayyana cewar a can inda aka fito su kan yi jinkirin zuwa wuraren da aka samu matsalar gobara, hasalima jama’a kan dauki lokaci suna jiran jami’ansu lamarin da ya bayyana a yanzu ya sha bamban domin sun magance wannan matsalar suna gudanar da aiki cikin hanzari yadda ya kamata ba tare da bata lokaci ba.

A kokarin ganin an fito da sababbin hanyoyi da dabarun bunkasa ayyukan Hukumar tare da tafiya da zamani kwatankwacin yadda Hukumomin Kashe Gobara a kasasehn duniya ke yi; Hukumar a Sakkwato ta bayyana cewar nan gaba kadan za ta fito da tsarin tafiya wuraren kashe gobara da motocin asibiti na tafi da gidanka domin bayar da agajin gaggawa ga wadanda suka samu raunuka a yayin ibtila’in gobara tare da kai su asibiti cikin hanzari kamar yadda Shugaban Hukumar ya bayyana tare da cewar abubuwan da ke haddasa gobara sune ganganci da rashin kiyayewa don haka yake kira ga al’umma da su rika lura.

Bugu da kari domin ganin ma’aikatan Hukumar sun samu horo domin gudanar da aiki a matakin kololuwa na kwararru, a lokaci zuwa lokaci Hukumar kan tura ma’aikatan ta a kwasa-kwasan dabaru da sanin makamar aiki a Kwalejin Kashe Gobara a Kano da Abuja a inda suke samun ingantaccen horo da sake samun horo kan yadda za a rika gudanar da aikin da suka fi iyawa, wayo da lakanta a cikin nasara.

A kan wannan Shugaban Hukumar Murtala Mohammed ya bayyana cewar suna da burin samar da Kwalejin Horas da Ma’aikatan Kashe Gobara a Cibiyar ta Daular Usmaniyya ta yadda idan haka ta cimma ruwa maimakon zuwa karbar horo a wajen jiha, ma’aikatan su za su rika samun horo a cikin gida kamar kuma yadda sauran jami’ai daga wajen jiha za su rika zuwa Sakkwato domin karbar horo.

A bisa ga dimbin asarar da ‘yan kasuwar Jihar Sakkwato suka yi a dalilin mummunar gobarar da ta afku a Tsohuwar Kasuwa da bukatar da ke akwai ta tallafawa wadanda lamarin ya shafa domin saukaka masu asarar da suka yi; Gwamnatin Jiha ta ware milyoyin kudade wadanda ta rarrabawa ‘yan kasuwar a wani dan kwarya-kwaryan taro a shekarar da ta gabata, tallafin da ba wai kawai yayi tasiri ga wadanda a ka baiwa ba, ya kuma kara bayyanar da Gwamnatin Tambuwal a matsayin mai jinkai da taimakon al’ummarta tare da share masu hawaye a lokaci mafi dacewa.

A kan kayan aiki da sinadaran kashe wuta kuwa, Shugaban ya bayyana cewar “Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya samar mana da dukkanin kayan aiki domin ganin aikin mu yana tafiya cikin tsanaki ba tare da wata matsala ba. Muna kuma da ma’aikata da ke kokari sosai amma duk da hakan muna bukatar karin ma’aikatan da za su taimaka ga gudanar da aikin kariya da daukin gaggawa ga al’umma.

Ya ce a shekarar da  ta gabata a Jihar Sakkwato, sun shaidi gobara 553 wadda ta zama silar asarar kadarori da dukiya na bilyan 3.1 a fadin jihar amma kuma sun yi nasarar kiyaye asarar kadarori na naira bilyan 4.1 a tsayin lokacin.

LEADERSHIP A Yau ta labarto cewar a watan Nuwamban shekarar da ta gabata a bisa ga muhimman nasarorin da Gwamnatin Tambuwal ta samu a sha’anin kashe gobara tare da tallafawa wadanda annobar gobara ta shafa a Jihar Sakkwato, hadakar Kwamitin Al’amurran Cikin Gida na Majalisar Dattawa da na Majalisar Wakilai tare da hadin guiwar Kungiyar Kiyaye Afkuwar Hadarin Gobara ta Kasa (FDPSAAN) sun karrama Gwamna Tambuwal da lambar girma ta 2017 domin yabawa kwazonsa na inganta Ayyukan Hukumar Kashe Gobara a Sakkwato.

 

 

Exit mobile version