‘Yan uwan wata budurwa ‘yar shekara 23 mai suna Nana Fiddausi Sa’idu da ke da zama a Unguwar Makera gudunmar Rigasa a Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, sun yi kira ga masu hannu da shuni, da su taimaka wa rayuwar buduwar, biyo bayan kamuwa da wata larura wanda hakan ya janyo halitta ta koma tamkar, ta karamar yarinya.
Wata kanwar mahaifiyarta mai suna A’i ta yi zargin cewa, Nana ta kamu da larurar ce, bayan da mahaifin Nana ya dauke ta daga gun dangin mahaifiyar ta ya kuma ya mayar da ita ga wata ‘yaruwarsa da ke a Jihar Kano.
- Kashi 67 Cikin 100 Na Ɗaliban Kaduna Sun Samu Nasara A WAEC – Kwamishinan Ilimi
- Ronaldo Da Messi Ne Kan Gaba A Jerin ‘Yan Wasan Da Suka Fi Karbar Albashi
Ta ce, lafiyar ta lau mahaifinta ya dauke ta daga wurinsu amma sai ta gudo daga gun ‘yaruwar ta sa daga Kano saboda ‘yar uwar uban, na yi mata mata horo da ruwan zafi.
A cewarta, Nana ta je tashar mota ta Kano ne, inda ta nemi taimakon mutane da su sanya a mota ta dawo Kadauna, suka dauko ta suka kawo ta gidanmu.
Ta ce, bayan da Nana ta kamu da larurar babu wata kulawa daga mahaifinta, ya yi wasti da ita, kuma ‘yanu wansa babu wanda ya damu da halin da take a ciki.
Ta ce, bayan kwana biyu ta fadi aka kaita asibitin Nasiha ba a cikin hayyacinta ba, aka kwantar da ita, a rika kiran mahaifinta a waya, daga baya ya zo ya iske, ana yi mata karin ruwa, sai ya cire robar karin ruwan har suka fara sa-insa da wata jami’ar asibitin, amma ya matsa sai da aka cire mata aka dawo da ita gida.
Ai ta ce, larurar ta koma mata kamar farfadiya, wanda duk inda take, sai ta fadi tana fisge-fisge, yanzu gashi mahaifinta ya rasu, kuma ‘yanuwansa, babu wanda ya damu da halin laruwar da take ciki.
Da aka tambaye ta ko sun sanar da hukuma lamarin ta ce, ba a sanar da hukuma ba, inda ta ce, tun ana yi mata magani, yanzu dai karfinsu ya kare, amma suna neman taimako don a ceto raywarta.
Shi ma Ibrahim Hannafi wanda yayan mahaifiyar Nana ne, ya zargi ‘yan uwan mahaifi da nuna halin ko in kula a kan larurar Nana, inda ya yi kira ga masu hali, da su taimaka a ceto raywar budurwar.
Ya ce, lokacin mahaifinsu yana raye, shi ne yake kulawa da halin da take ciki amma ya ce, mu kyale, ‘yan uwan mahaifinta da halin sun nuna ko in kula dangane da larurar ta, kuma bai bar su mun dauki wani mataki ba a lokacin da yake raye.
Shi kuwa Malam Anas Musa dan kungiyar kare hakkin ‘yan’Adam cewa ya yi, an zalunci yarinyar, duba da yadda dangin mahaifinta suka yi watsi da ita, suka bar nauyinta a gun dangin uwarta, inda ya ce, a kungiyance, za mu bi wa Nana kadin tauye mata ‘yancinta.