• English
  • Business News
Friday, May 23, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yajin Aikin ASUU: Mece Ce Makomar Daliban Jami’o’in Nijeriya? (Ra’ayi)

by Muhammad Bala Garbasu
3 years ago
in Rahotonni
0
ASUU
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Yau kimanin wata biyar ke nan daliban da ke jami’o’i a Nijeriya suke zaune a gidajensu saboda yajin aikin da Malaman jami’o’i suka tsunduma. Shin mece ce makomar wadannan daliban?

A ranar Litinin 14 ga watan Fabrairun wannan shekarar ta 2022 kungiyar Malaman jami’o’in Nijeriya, wato ASUU, ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamnatin kasar nan na tsawon wata guda; kafin ta sake kara wasu watanin ukun.

  • Ya Kamata Buhari Ya Gaggauta Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU – Femi Falana

ASUU ta shiga yajin aikin ne sakamakon abin da ta kira da gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da yarjejiyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatu a jami’o’in kasar.

Binciken da na yi dangane da yawan tafiyar ASUU yajin aiki, ya nuna sau goma sha shida (16) kungiyar tana tafiya yajin aiki tun bayan komawar Nijeriya mulkin demokradiyya kamar haka:
1. Yajin aikin wata biyar a shekarar 1999
2. Yajin aikin wata uku a shekarar 2001
3. Yajin aikin sati biyu a shekarar 2002
4. Yajin aikin wata shida a shekarar 2003
5. Yajin aikin sati biyu a shekarar 2005
6. Yajin aikin sati daya a shekarar 2006
7. Yajin aikin wata uku a shekarar 2007
8. Yajin aikin sati daya a shekarar 2008
9. Yajin aikin wata hudu a shekarar 2009
10. Yajin aikin wata biyar a shekarar 2010
11. Yajin aikin wata biyu a shekarar 2011
12. Yajin aikin wata biyar da rabi a shekarar 2013
13. Yajin aikin wata daya a shekarar 2017
14. Yajin aikin wata uku a shekarar 2018
15. Yajin aikin wata tara a shekarar 2020
16. Sai kuma yajin aikin da aka tsunduma a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairun wannan shekarar ta 2022 wanda ba a san karshensa ba tukuna.

Shin me yake kawo wannan yajin aikin kuma daga ina matsalar take?
Nijeriya kasa ce da ke da mabiya addinai daban-daban, manyan daga cikinsu, su ne, addinin Islama da Kiristiyaniti wadanda suka shigo kasar tun shekaru aru-aru kafin zuwan Turawan mulkin mallaka.

Labarai Masu Nasaba

Gwamna Umar Namadi Ya Dauki Matakan Kai Jihar Jigawa Babban Matsayi

Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro

Tun daga wannan lokaci ake samun hanyoyin ilimantar da jama’a.
Zuwan kungiyoyin mishan-mishan Nijeriya a tsakanin shekarun 1842 zuwa 1914 ne ilimin boko ko kuma na zamani ya shigo kasar; yayin da a tsakanin wadannan shekaru kimanin kungiyoyin mishan 10 ne suka shigo suna ayyuka daban-daban da suka hada da ilmantar da jama’a wanda suka baiwa karfi sosai. Tun daga wannan lokacin aka giggina makarantu ake daukar jama’a musamman yara domin ba su ilimin.

Bayan darrusa 4 da ake koyarwa a makarantun, wadanda suka hada da: karatu da rubutu da lissafi da kuma addininsu, wato Kiristanci da aka horas da su ta yadda za su samu aikin yi kamar koyarwa da wa’azi a majami’u da tafinta.

A shekarar 1857 aka gina makarantar CMS (Church Missionary Society) grammar school da ke jihar Legas.
Ilimin Boko bai samu karbuwa a Arewacin Nijeriya ba (a wancan lokacin), saboda al’ummar yankin suna tsoran ka da ya gurbata musu addininsu.

An kiyasce cewa, a shekarar 1914, an samu makarantun Arabiya kimanin 25,000 a fadin Arewacin Nijeriya, wanda hakan ne ya jawo rashin karbuwar ilimin Boko a yankin. Kodayake, kungiyoyin mishan sun samu karbuwa a wasu sassan yankin, inda suka gina makarantunsu.

A tsakanin 1882 zuwa 1950 ne shuwagabannin yankunan kasar suka fito da ka’idojin yadda za a ringa koyar da al’ummarsu.

A tsakanin 1952 zuwa 1960 dukanin yankunan uku suka shimfida sabbin dokokin tsarin koyarwa a yankunansu, wanda aka fara gwadawa da shirin ilimin bai-daya (free education) na firamare. A shekarar 1955 aka fara gabatar da shirin a Yammacin kasar, a shekarar 1957 kuma aka fara a Gabashi.

A shekarar 1952 ne aka kafa hukumar shirya jarabbawa ta kasashen Yammacin Afirka, wato WAEC (West African Edamination Council).

Bayan da Nijeriya ta samu ‘yancin kanta a ranar daya ga watan Oktoban 1960, gwamnatin tarayya ta kaddamar da bude jami’o’i 6 wadanda suka hada da:
1. Jami’ar Ibadan wadda aka fara kafa ta a shekarar 1948.
2. Jami’ar Nsukka a shekarar 1960.
3. Jami’ar Ile-Ife a shekarar 1961.
4. Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1962.
5. Jami’ar Legas a shekarar 1962.
6. Jami’ar Benin a shekarar 1970.
Duka wadannan da nufin bunkasa ilimi tare da magance wasu matsaloli da gwamnatin wancan lokaci ta fara hanga. Bayan wadannan jami’o’in, gwamnati ta giggina wasu manyan makarantun da nufin samar da ilimi a wasu bangarorin kamar fasaha da kere-kere.

A lokacin da Nijeriya ta samu bunkasar tattalin arziki ta hanyar man fetur, gwamnatin tarayya ta bullo da shirin ilimin bai-daya na ba da ilimi kyauta a makarantun furamare.

Sai dai ba a je ko ina ba, shirin ya wargaje, saboda rashin kyakkyawan tsari da isassun kudade.

A shekarar 1999 ne gwamnatin tarayyar ta sake kaddamar da wani shirin ba da ilimi kyauta da nufin bunkasa ilimin da aka yi na farkon.

Sai dai kuma har yanzu ba a kai ga cimma burin bunkasa ilimi a kasar ba, saboda wasu matsaloli ko dalilai da kasar ke fuskanta. Matsalolin da ilimi ke fuskanta a Nijeriya sun hada da:
1. Talauci: Nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnati tun daga tarayya har zuwa kananan hukumomi ta bai wa al’ummarta ilimi a kalla na firamare, sai dai kuma ba a ko ina ne gwamnatin ke sauke wannan nauyi ba, musamman ma a yankunan karkara, inda a wurare da dama babu ko da dakin karatu; inda aka samu kuma im ma babu Malamai ko kuma kayayyakin aiki.

A irin halin da kasar ke ciki na tattalin arziki, jama’a da dama na cikin talauci don haka ba za su iya daukar dawainiyar karatun ‘ya’yansu ba, wanda hakan ya sa ‘ya’ya da dama ba sa zuwa makarantu.

2. Tattalin Arziki: Bayan talauci da ke kawo koma baya ga ilimi a Nijeriya (musamman a yankin Arewa), batun tattalin arziki da zafin nema da dogaro da kai ya kasance wata babbar matsala da fannin ilimi ke fuskanta a kasar; musamman a gabashin kasar. A wancan yankin, ba kasafai ‘ya’ya maza ke kammala karatun firamare ba, inda suka fi mai da hankali wajen kasuwanci.

‘Ya’ya mata ne kadai wasu ke kaiwa har zuwa jami’a. Wannan kuwa ya samo asali ne tun lokacin yakin basasar da aka yi a kasar (yakin Biyafara), lokacin da tattalin arzikin yankin ya shiga halin ni-‘ya-su.

A bangaren Arewacin kasar kuwa, matsalar rashi ko talauci ke sa iyaye gwanmacewar dora 96+-wa ‘ya’yansu talla a madadin turasu makaranta, wannan kuwa ba ga mata kadai ba, har ga maza, wanda hakan ya taimaka wajen rashin zuwan dubban ‘ya’ya makarantu sannan kuma ya yi sillar lalacewar wasu daga cikinsu (musamman ‘ya’ya mata).

3. Al’ada ko Addini: Batun al’ada ko addini wani babban matsala ne da ke fuskantar fannin ilimi a Nijeriya (musamman a Arewa). Wannan kuwa ya hada da yi wa ‘ya’ya mata auren wuri, abin da ya sa ake samun ‘ya’ya maza na zuwa makaranta fiye da mata. Yawancin al’ummar yankin (Arewa) na kyamatar cudanyar maza da mata a wuri guda.

4. Malamai da kayan aiki: Babbar matsalar da a yanzu haka fannin ilimi ke fuskanta a Nijeriya, shi ne, rashin kayayyakin aiki wanda ya kamata gwamnati ta samar a makarantu. Wannan shi ne babban abin da ke jawo karancin malamai a makarantu, kama daga firamare har zuwa jami’o’i.

5. Rashin biyan bukatun Malamai yadda ya kamata: Bayan rashin kayayyakin aiki, akwai kuma rashin biyan bukatun malamai yadda ya kamata da gwamnatin ke yi, wanda hakan ne ke kawo yawan yajin aiki tare da kuma sa kwararrun Malaman makarantu musamman daga shekarun 1980 zuwa 1990, lokacin da gwamnati ta fito da shirinta na tsuke bakin aljihu, wato SAP, barin kasar zuwa wasu kasashen waje.

Ana kukan targade, sai ga karaya, wanda ya yi sanadiyar rufe makarantun kasar gaba daya a shekarun baya (wato batun annobar Korona Bairos), wanda ta kai ga dalibai sun kusan share shekara guda a gidajensu ba tare da zuwa makarantu ba.

A irin wannan yanayin da ilimi ke fuskantar wadannan matsaloli a Nijeriya, ana zuwa makarantun ma yaya aka kare ballatana kuma ba a zuwa?
Bayan lafawar wannan annobar wacce ta ba da damar bude makarantu, ko shekara ba a yi ba, kungiyar Malaman jami’o’i ta tsunduma yajin aiki, wanda ya jefa dalibai da dama cikin mummunan yanayi. Shin mece ce makomar wadannan daliban? Ya ya gobensu zai kasance idan aka ci gaba da tafiya a haka?
Da wannan nake kira ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, ta yi wa Allah da Manzonsa (Sallalahu alaihi wasalam), ta yi duba ga makomar wadannan daliban, ta zauna da Malaman jami’o’i su sassanta domin dakile wannan yajin aiki.

Ci gaba da wannan yajin aikin babbar barazana ce ga makomar ilimin kasar da kuma rayuwar wadannan daliban wadanda su ne manyan gobe kuma magina kasar.

A karshe ina rokon Ubangiji Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya mai dorewa, ya kuma ba mu shuwagabannin nagari masu kaunar mu da kaunar ci gabanmu, Amin.

Dalibinku, Mohammed Bala Garba, Maiduguri. 09042923950, 08098331260.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Dan Takarar Sanatan APC A Abiya, Kelvin Ugboajah Ya Mutu

Next Post

An Cafke Mutumin Da Ya Kashe Tsohuwa Ya Sayar Da Sassan Jikinta A Ogun

Related

Gwamna Umar Namadi Ya Dauki Matakan Kai Jihar Jigawa Babban Matsayi
Rahotonni

Gwamna Umar Namadi Ya Dauki Matakan Kai Jihar Jigawa Babban Matsayi

1 month ago
Janar Tiani Ya Fara Sabon Mulkin Shekaru Biyar A Nijar
Rahotonni

Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro

1 month ago
An Gudanar Da Taron Zaman Lafiya Tsakanin Manoma Da Makiyaya
Rahotonni

An Gudanar Da Taron Zaman Lafiya Tsakanin Manoma Da Makiyaya

1 month ago
Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa
Rahotonni

Amurka Ta Sayi Kayayyakin Nijeriya Na Dala Miliyan 643 A Wata 2 – Rahoto

1 month ago
Gwamnoni 20 Na Fuskantar Matsin Lambar NULGE Kan Rashin Aiwatar Da Mafi Karanci Albashi
Rahotonni

Gwamnoni 20 Na Fuskantar Matsin Lambar NULGE Kan Rashin Aiwatar Da Mafi Karanci Albashi

1 month ago
Tinubu
Manyan Labarai

Yadda Tinubu Ya Shirya Wa Kansa Mafitar Siyasa Kafin Zaben 2027

2 months ago
Next Post
tsohuwa

An Cafke Mutumin Da Ya Kashe Tsohuwa Ya Sayar Da Sassan Jikinta A Ogun

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Sama Jannatin Shenzhou-20 Sun Kammala Aiki A Wajen Tashar Sararin Samaniyar Kasar Sin

‘Yan Sama Jannatin Shenzhou-20 Sun Kammala Aiki A Wajen Tashar Sararin Samaniyar Kasar Sin

May 22, 2025
Ba Zai Yiwu Amurka Ta Kafawa Chips Kirar Kasar Sin Wani Shinge Ba

Ba Zai Yiwu Amurka Ta Kafawa Chips Kirar Kasar Sin Wani Shinge Ba

May 22, 2025
Ganduje Ya Zargi Gwamna Yusuf Da Ɗaukar Nauyin Zanga-zanga A Kano

‘Yan PDP Na Komawa APC Ne Saboda Jam’iyyarsu Na Jin ƙamshin Mutuwa – Ganduje

May 22, 2025
Masanan Najeriya Sun Bayyana Muhimmancin Hadin Gwiwar Afirka Da Sin A Fannin Tinkarar Kalubalen Harajin Kwastam Na Amurka

Masanan Najeriya Sun Bayyana Muhimmancin Hadin Gwiwar Afirka Da Sin A Fannin Tinkarar Kalubalen Harajin Kwastam Na Amurka

May 22, 2025
Modric Zai Bar Real Madrid Bayan Kammala Gasar Cin Kofin Duniya Na Kungiyoyi

Modric Zai Bar Real Madrid Bayan Kammala Gasar Cin Kofin Duniya Na Kungiyoyi

May 22, 2025
Yawan Wutar Lantarkin Da Sin Ke Iya Samar Ta Amfani Da Karfin Ruwa Ta Kai Matsayin Koli A Duniya

Yawan Wutar Lantarkin Da Sin Ke Iya Samar Ta Amfani Da Karfin Ruwa Ta Kai Matsayin Koli A Duniya

May 22, 2025
Za Mu Riƙe Wa Minista Tijjani Muƙaminsa Bayan Hamɓarar Da Tinubu A 2027 – El-Rufai 

Za Mu Riƙe Wa Minista Tijjani Muƙaminsa Bayan Hamɓarar Da Tinubu A 2027 – El-Rufai 

May 22, 2025
Darussan Koyi Daga Salon Bunkasa Kasa Na Sin

Darussan Koyi Daga Salon Bunkasa Kasa Na Sin

May 22, 2025
Ƙungiyar ’yan Majalisar Dokokin Ƙasa Ta APC Ta Amince Da Takarar Tinubu A Zaɓen 2027 

Ƙungiyar ’yan Majalisar Dokokin Ƙasa Ta APC Ta Amince Da Takarar Tinubu A Zaɓen 2027 

May 22, 2025
Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Faransa

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Faransa

May 22, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.