Rarrabuwar kawuna ta ya haifar da cikas ga samun nasarar yajin aikin gargadi na kungiyar kwadago (NLC) na kwanaki biyu domin matsin lamba ga gwamnatin tarayya ta gaggauta aiwatar da tsare-tsaren rage radadin cire tallafin man fetur.
A duk fadin tarayyar kasar nan kungiyoyin TUC da NLC sun samu rarrabukar kawuna kan yajin aikin da suka shirya tun daga Talata har zuwa Laraba na wan-nan mako.
- An Samu Nasarori Sama Da 1100 A Gun CIFTIS Na Shekarar 2023
- Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Da Jam’iyyar APM Ta Shigar Kan Ingancin Shettima
TUC ta ce tana adawa da yajin aikin ne saboda ba zai haifar da da mai ido ba.
A ranar Litinin an rufe dukkan ofishoshin gwamnati da suka hada da ma’aikatu da hukumomi, bayan da ma’aikatan Jihar Kwara suka tsunduma yajin aiki kamar yadda kungiyar NLC ta ba da umarni.
Amma masu zaman kansu sun bude wuraren kasuwancinsu don gudanar da ayyukansu na yau da kullun ba tare da wani tsangwama ba.
Wasu bankunan a Ilorin, babban birnin jihar suma sun gudanar da ayyukansu.
LEADERSHIP ta bayyana cewa, ma’aikatan da aka gani a ofisoshin da ke sakatari-yar jihar su ne ‘yan kungiyar TUC da suka ce ba sa cikin yajin aikin, yayin da sau-ran ma’aikatan da ke karkashin NLC suka rufe suka koma gida gaba daya bisa bin umarnin kungiyar.
A Babban Birnin Tarayya (Abuja) ya samu cikas daga wasu ma’aikatun da kuma hukumomin gwamnati a yajin aikin kwanaki biyu da kungiyar kwadago ta Nijeriya ta ayyana a fadin kasar nan.
A lokacin da LEADERSHIP ta ziyarci sakatariyar gwamnatin tarayya tare da wasu manya-manyan wurare irin su FCTA da FCDA, da kuma wasu bankunan yankin, an gano cewa kadan daga cikin wadannan wuraren suka bi yajin aikin, yayin da wasu kuma ba su bi ba kwata-kwata.
Shugaban kungiyar na Jihar Kuros Ribas, Kwamared Monday Ogbodum, ya yi Al-lah-wadai da yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da shugabannin kungiyar NLC suka shiga, inda ya bayyana shugabancin kungiyar a matsayin maras alkimla.
Ogbodum, wanda ya zama shugaban kungiyar manyan ma’aikatan gwamnati a Jihar Kuros Ribas, ya bayyana cewa kungiyar TUC ba ta goyon bayan yajin aikin saboda NLC ba ta bi ka’ida ba kafin ta kira mambobinta da su shiga yajin aikin gargadi na kwanaki biyu, wanda siffanta lamarin da bai cika ka’ida ba.
Shugaban na TUC ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da LEADERSHIP a wata tattaunawa ta wayar tarho a jiya bayan NLC ta bukaci ma’aikatan jihar su zauna a gida.
“Domin bin tsarin da ya dace, mun ware makonni biyu, a yanzu haka muna da wa’adin kwanaki bakwai kafin daga bisani mu umarci ma’aikata su shiga yajin aiki ko kuma akasin haka.
“Muna sane da cewa ‘yan Nijeriya na shan wahala, amma yajin aiki ba shi ne zai kawo mafita ba. TUC ta kasance ‘yan gaba-gaba wajen warware lamarin na tun-karar gwamnatin tarayya.
“Tattaunawa shi ne mafita. Ta hanyar tattaunawa ne shugabannin NLC da TUC da gwamnatin tarayya suka kai wa jahohi tallafin naira biliyan 5. Mun yi maganar gyaran matatun mai, ba zai zama abun da za a iya warwarewa lokaci guda ba. Shugaban kasa ya bayar da sanarwar cewa matatun man za su fara aiki zuwa Dis-amba 2023.
Yajin aikin dai ya samu tangarda a Jihar Legas, yayin da ma’aikatan gwamnati da ma’aikatu masu zaman kansu suka yi watsi da yajin aikin, wanda jama’a sun ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum yadda ya kamata, kamar yadda LEADERSHIP ta bayyana.
Sakamakon binciken da LEADERSHIP ta yi ya nuna cewa yajin aikin ya fi tasiri ga ma’aikatan hukumar da ke kula da bakin teku, domin an hana ma’aikata shiga tashoshin jiragen ruwa, yayin da bankuna da kamfanonin inshora da sauran masu gudanar da aiki a sassan kasar nan suka ci gaba da gudanar da ayyukansu nay au da kullum duk da kokarin talasta musu da wasu ‘yan kungiyar kwadago suka yi domin dakatar da su.
Tun da kiran yajin aikin bai hada da zanga-zangar a kan tituna ba, yajin aiki ne wanda ke nufin ma’aikata gwamnatin tarayya da na jihohi da kuma na kananan hukumomi kar su tafi wuraren aikinsu.
A halin da ake ciki, binciken LEADERSHIP ya ruwaito cewa kofofin shiga Sakatari-yar Alausa da ke Ikeja a Jihar Legas a bude suke kamar yadda aka saba domin shigowar ma’aikata.