Manyan jam’iyyun adawa a kasar nan na ci gaba da caccakar shugabannin jam’iyyar APC saboda goyon bayan tazarcen Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan damar samun wa’adin mulki na biyu.
Rahotanni na cewa manyan jiga-jigan APC sun yi amfani da duk hanyoyin da suke da su domin yaba wa gwamnatin Tinubu da kuma goyon bayan sa don sake tsayawa takara a 2027.
- Yawan Wutar Lantarkin Da Sin Ke Iya Samar Ta Amfani Da Karfin Ruwa Ta Kai Matsayin Koli A Duniya
- Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Man Fetur
A lokacin da shugabannin APC a Arewa Maso Yamma suka goyi bayan shugaban kasar a karshen mako a Kaduna, jam’iyyun adawa sun nuna rashin jin dadinsu game da wannan lamari.
Shugaban APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da gwamnonin da ke cikin jam’iyyar daga yanki, ciki har da Uba Sani na Jihar Kaduna, Nasir Idris na Kebbi, da Umar Namadi na Jigawa sun halarci taron.
Sauran sun hada da shugaban majalisar wakilai, Dakta Tajudeen Abbas da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I Jibrin, ministocin daga yanki, shugabannin kananan hukumomin APC, masu wakiltar jihohi da na kasa tare da shugabannin hukumomin tarayya.
An dai fara goyon bayan tazarcen Tinubu a wurin taron lokacin da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya ce babu wani gurbi a fadar shugaban kasa a 2027.
Barau ya ce, “A bayyane yake a 2027, za mu sami gagarumar nasara, In Sha Allah. Don haka, mu ci gaba da hanyar da muke kai. Mu hada kai da juna, mu yi aiki tare da shugaban kasa, mu yi aiki tare da kowa, mu hada kai a tsakaninmu don samun nasarar da ake bukata.”
Sanata Barau ya ci gaba da cewa sauya shekan wasu shugabannin jam’iyyun adawa zuwa APC ya kasance sakamakon aikin Shugaba Tinubu a cikin shekaru biyu kawai da ya shafe a kan karagar mulkin Nijeriya.
Kazalika, Ganduje ya ce Shugaba Tinubu na da kishin ci gaban Arewa Maso Yamma da dukkan yankin Arewa da ma Nijeriya gaba daya, don haka ya cancanci wa’adin mulki na biyu.
Ya ce yi matukar yin kokari ta hanyar wasu ayyukan da gwamnatisa ta bijiro da su, tun daga kan samar da kayayyakin more rayuwa har zuwa bunkasa bangaren noma a yankin Arewa.
Ganduje ya jaddada cewa kafa ma’aikatar bunkasa yankin Arewa Maso Yamma alama ce a fili na cewa shugaban kasa yana son yankin Arewa Maso Yamma.
Haka kuma, Gwamna Uba Sani ya ce yankin Arewaci Maso Yammaci ya bunkasa a karkashin jagorancin Shugaban kasa Tinubu.
“Shugaba Tinubu ya karbi iko ne lokacin da al’amuran kasarmu suka kasance mafi munin kalubale a tarihinta,” in ji shi.
Ya yaba da canje-canje masu amfani na Tinubu, yana cewa, “Shugaban ba ya jin tsoron yanke shawara masu wahala. ‘Yan Nijeriya ma sun fara fahimtar cewa Mai Girma Shugaba yana da kyawawan manufofi ga kasarmu.”
A nasa jawabin, shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya ce ficewar wasu daga jam’iyyun adawa zuwa APC ya nuna karuwar yarda da ‘yan Nijeriya ke nuna wa jam’iyyar da shugabancinta, amma ya jaddada cewa jam’iyyar dole ne ta karfafa yawan masu goyon baya tun daga mataki na kasa.
A cikin martaninsa, shugaban jam’iyyar ADC, Dakta Ralphs Okey Nwosu, ya ce Tinubu bai cancanci yin tazarce ba.
Nwosu, a wata tattaunawa ta wayar tarho da manema labarai, ya ce idan aka duba matsayin shugaban kasa bisa kashi, yana iya samun kashi 10 kacal cikin dari sakamakon rashin tsinana abun kirki na shugabancin kasar nan.
Da yake magana kan goyon bayan shugaban kasa daga masu ruwa da tsaki na APC a Kaduna, Nwosu ya ce ‘yan adawa ne kadai za su iya ceto kasar nan, yana mai cewa idan har APC ta ci gaba da mulki a 2027, mutane da yawa daga cikin ‘yan Nijeriya za su mutu da yunwa.
Amma jam’iyyar SDP ta ce ‘yan Nijeriya za su tantance wane ne zai yi nasara a zaben shugaban kasa na 2027 idan lokaci ya yi.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar, Araba Rufus Aiyenigba, ya shaida hakan, inda ya ce, “Mutanen Nijeriya ne za su tantance wanda zai zama shugaban kasan Nijeriya a 2027, ba shugabannin APC ba,” in ji Aiyenigba.
Sakataren yada labarai na NNPP, Ladipo Johnson, ya ce goyon baya daga cikin gida na jam’iyya na da karancin tasiri wajen gwada gwazon gwamnati.
Shi kuwa wani mamba na kwamitin zartarwa na jam’iyyar PDP, Tim Osadolor ya ce goyon bayan Shugaba Tinubu ba zai haifar da komai ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp