Fitaccen mai harkokin siyasa, Salihu Lukman, ya ce jam’iyyun adawa na iya cimma matsaya kan ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya kwanaki kaɗan kafin zaɓen 2027.
Lukman ya ce jam’iyyun na tattaunawa domin guje wa rarrabuwar ƙuri’u da kuma ƙara samun damar kayar da jam’iyyar APC mai mulki.
Ya bayyana rashin amincewa da juna tsakanin shugabannin jam’iyyun adawa a matsayin babban ƙalubalen da ke hana su cimma matsaya.
Ya kuma buƙaci magoya bayan Peter Obi, Atiku Abubakar da sauran ’yan siyasa su fifita muradun Nijeriya a kan burinsu na siyasa.
Lukman ya ce jam’iyyun za su kuma amince da muhimman manufofi da suka shafi tattalin arziƙi, ilimi da tsaro kafin zaɓen ɗan takarar da za su mara wa baya.
Ya ƙara da cewa ɗan takarar da za su zaɓa zai iya fitowa daga jam’iyyar ADC, wata jam’iyya daban ko kuma sabuwar jam’iyyar da za a kafa ta hanyar haɗin gwiwar jam’iyyun adawa.














