Jakadan kasar Sin kan harkokin kwance damarar makamai Li Chijiang, ya yi kira ga kasashen duniya su hada hannu wajen magance hadura da barazanar makaman nukuliya.
Li Chijiang ya bayyana haka ne jiya Juma’a, yayin wata muhawara kan makaman nukuliya, a taron kwamitin kwance damarar makamai da tsaron duniya na zaure na 81 na MDD.
Ya ce matsayin kasar Sin na goyon bayan haramta amfani da makaman nukiliya baki daya ta hanyar lalata su yana nan daram, kuma manufarta ta kaucewa zama ta farko wajen amfani da makaman nukiliya ba ta sauya ba, haka kuma ba ta kasa a gwiwa a kokarinta na tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a duniya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














