‘Yan Banga Sun Kashe ‘Yan Bindiga 30 A Jihar Katsina

Garkuwa

Daga Sulaiman Ibrahim

Rahotanni daga Jihar Katsina sun bayyana cewa wasu ‘yan banga a kauyen Majifa da ke karamar hukumar Kankara sun yi nasarar kashe akalla ‘yan bindiga 30 da suka addabe su sakamakon kwantar baunar da suka musu a daren litinin din da ta gabata.

Jaridar Daily Trust ta ce, ‘yan sa kan tare da mazauna kauyen sun samu labarin shirin kai musu hari, abinda ya sa suka yi shiri, kuma sun yi sa’ar kashe wasu daga cikin maharan.

Wani shaidar gani da ido ya ce maharan cikin dare bisa ababan hawa, wasu harda rakuma sun koma inda suka kwashe gawarwakin yan uwan su da aka kashe.

Jaridar ta ce an samu irin wannan artabu a kauyukan ‘yan marafa da Mununu da ke karamar hukumar Faskari inda aka kashe mutane da dama.

Exit mobile version