‘Yan bindiga sun kashe manoma bakwai tare da jikkata wasu da dama a wani sabon hari da suka kai garin Otobi-Akpa da ke ƙaramar hukumar Otukpo a Jihar Benuwe da yammacin ranar Talata.
Harin ya jefa jama’ar garin cikin fargaba, inda da dama suka fara barin gidajensu domin neman mafaka.
- Za A Watsa Shirin Bidiyon “Bayanan Magabata Dake Jan Hankalin Xi Jinping” Na Harshen Malay
- Gazawar Gwamnati Kan Kiyaye Rayuka Da Dukiyoyi: Gwamnan Filato Ya Nemi Yafiyar Al’ummar Jihar
Wani mazaunin garin mai suna Alechenu ya ce maharan da ake zargin makiyaya ne sun shiga garin da misalin ƙarfe 6:30 na yamma, lokacin da mafi yawan mutane ke dawowa daga gonaki.
Ya ce suna zuwa, sai suka fara harbe-harbe da ƙone gidaje.
Wani ganau, Elaigwu Idoko, wanda ya shiga cikin tawagar tsaro wajen binciken waɗanda suka ɓace, ya tabbatar da cewa an gano gawarwakin mutum bakwai zuwa yanzu.
Ya ce suna ci gaba da bincike a cikin dazuka da ke kusa da garin.
Ɗan majalisar dokokin Jihar Benuwe mai wakiltar mazaɓar Otukpo-Akpa, Kennedy Angbo, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce harin ya faru da misalin ƙarfe 5:30 na yamma kuma jama’a da dama sun tsere daga garin saboda tsoro.
Wani mazaunin Otobi, Edwin Emma, ya ce wannan ne karo na biyu da ake kai musu hari cikin wata guda.
“Matata da ’ya’yana sun tsere a kafa yanzu haka. Muna buƙatar taimako,” in ji shi.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yansandan Jihar Benuwe, Catherine Anene, bai yi nasara ba domin wayarta a kashe ta ke.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp