Wasu mazauna kauyukan Kango da Dangulbi a karamar hukumar Maru a jihar Zamfara, sun ce yaran dan bindiga Damina sun kashe mutane 18 da safiyar ranar Lahadi.
Mutane da dama da suka gudu daga kauyukan a dalilin farmakin sun gaza dawowa mahallansu.
- 2023: Ka Kula da Lafiyarka, Kwankwaso Ga Tinubu
- https://hausa.leadership.ng/2023-ka-kula-da-lafiyarka-kwankwaso-ga-tinubu/
Karamar hukumar Maru na ci gaba da fuskantar munanan hare-haren ‘yan bindiga.
Wani shugaban yankin da ya bukaci kar a bayyana sunansa, ya ce an birne mutane 18 din bisa koyarwar addinin musulunci.
Wani mutum mai suna Shehu Ismaila, daga yankin Maru, ya ce an kashe mutane 13 a Dangulbi sannan aka kashe biyar daga Kango.
Ismaila ya ce ‘yan bindigar sun fara zuwa kauyen Kango ne kafin nan suka je Dangulbi inda suka kashe mutane suna aiki a gonakinsu.
“An kashe mutane shida a wajen gari ragowar shidan kuma an kashe su a cikin kauye. Wadanda aka kashe da safe sun fita aiki gona don su dawo gida da wuri don yi bikin sallah,” in ji sa.
Kakakin ‘yan sandan jihar, Mohammed Shehu bai ce komai a kan harin ba, kuma bai daga kiran waya da aka masa ba.