’Yan bindiga sun kai hari garin Dukura, da ke ƙaramar hukumar Kebbe a Jihar Sokoto, inda suka kashe mutane biyu tare da kwashe dabbobi da babura na mazauna yankin.
Lamarin ya faru ne a safiyar Litinin, bayan ’yan bindigar sun tare hanyar da ke haɗa al’ummomin yankin da kasuwar Tambuwal.
Rahotanni sun ce maharan sun kwashe shanu, raƙuma, tumaki da kuma babura na wasu masu sana’ar achaba kafin jami’an tsaro su isa wurin.
Harin ya ƙara haifar da fargaba a Dukura, Dalijan da sauran ƙauyukan da ke cikin gundumar Girkau, ciki har da Zugu, Indire, Mazoji, Tungar Kabawa, Runtuwa, Jabga da Sabon Garin Zugu.
Jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ’Yansandan Jihar Sokoto, DSP Ahmed Rufai, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce rundunar ta samu bayanai kan harin tare da tura jami’anta zuwa yankin.
ADVERTISEMENT













