An gabatar da dimbin sabbin kayayyakin dake wakiltar sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, kamar mutum-mutumin injuna masu fasahar Kungfu, da na’urorin da aka kera domin taimakawa masu fama da matsalolin tafiya, da gilashin da ke amfani da fasahar AI, wadanda ke iya fassara da daukar hoto, a yayin bikin baje kolin hada-hadar cinikayya mafi girma da ake gudanarwa a kasar Sin, wanda aka fi sani da Canton Fair, lamarin da ya nuna himmar da aka yi wajen sabunta kayayyakin da ake nunawa yayin bikin na Canton Fair.
To ko ta yaya aka kai ga dada sabunta kayayyakin da ake nunawa a yayin bikin da a bana ke cika shekaru 70 da kaddamarwa?
Dalili na farko shi ne, kokarin da kasar Sin ke yi wajen ci gaba da yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha, da kuma raya sabon karfi na neman bunkasa. A ‘yan shekarun nan, kamfanonin kasar Sin da dama sun hada kafar intanet ta masana’antu da fasahar AI, cikin tsarin samar da kayayyaki, lamarin da ya janyo hankalin yan kasuwa daga sassan duniya. Ban da haka kuma, Sin tana da cikakken tsarin masana’antu, wanda ke tabbatar da samar da sabbin kayayyaki a kai a kai, tare da daidaita kayayyakin da aka kera a kasar Sin da bukatun kasuwannin duniya yadda ya kamata. Haka zalika, yadda kasar Sin ke ci gaba da kara bude kofa ga waje, da kafa dandalin hadin gwiwar tattalin arziki, da cinikayya mai inganci a tsakanin kasa da kasa dake dogaro ga Canton Fair, sun samar da karin damammakin samun sakamako mai gamsarwa ga dukkan bangarorin da ke harkar kasuwanci a duniya.
Cikin shekaru 70 da suka gabata, bisa bunkasar kasar Sin, da yadda ta kara bude kofa ga waje, an ci gaba da sabunta kayayyakin da ake nunawa yayin Canton Fair, amma aniyar kasar ta kafa wannan dandali ba ta sauya ba, wato Hada kan kasa da kasa, domin cimma moriyar juna. A nan gaba kuma, Yayin da ake ci gaba da gudanar da shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 15, kasashen duniya za su kara fahimtar kudurin kasar Sin na inganta manufar bude kofa ga waje, da kuma fadada fannonin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasa da kasa, wanda zai amfani dukkan bangarorin da abin ya shafa. Hakan ya nuna cewa, Canton Fair ba zai kare ba, kuma labarin hadin gwiwa da cimma moriyar juna a tsakanin kasa da kasa na ci gaba da bayyana. (Mai Fassara: Maryam Yang)














