Connect with us

LABARAI

Yan Gundun Hijira A Katsina Sun Samu Tallafin Magani Daga Rundunar Sojin Sama

Published

on

Rundunar sojin sama ta fara bayar da magani kyauta ga yankuna 20 da harin ‘yan bindiga ta rusta dasu a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Haka kuma rundunar ta raba wa al’ummar yankin kayan abinci da sauran kayayyakin bukatu ga masu gudun hijira a yankin.

Shugaban Rundunar Sojin Saman, Air Marshal Sadikue Abubakar, ya kaddama da shirin ranar Laraba a sansanin ‘yan gudun hijirar a garin Faskari.

Group Capt. Ali Tanko, ya wakilici shugaban rundunar sojin saman, ya kuma kara da cewa, cikin magungunan da za a bayar sun hada da cutar Maleriya, Kanjamau da Ciwon Suga da kuma Ciwon Hanta da kuma sauran cuttuka.

Abubakar ya ce, wannan na daga cikin gudunmawar rundunar don rage wa ‘yan gudun hijirar wahalhalun da suke fuskanta musammna ganin irin yadda ‘yan ta’adda suka farmakesu.

“Haka kuma tallafin zai taimaka wajen kara dankon zumunci a tsakanin sojin da fararen hula a yankin.

“Sojojin suma wani bangare ne na a’lumma don kuwa dole wata rana su za su gama aikinsu su dawo a cikin jama’a su zauna tare da sauran jama’a,” inji shi.

Bayani ya kuma nuna cewa, rundunar ta raba wa al’umma gidajen sauro da maganin tsutsar ciki musamman ga mata masu juna biyu a yara kanana.

Advertisement

labarai