Kungiyar jin dadin matasan ‘yan kasuwar Arewacin Nijeriya ta kasa mai helkwata a cikin birnin Lagos ta kaddamar da sabuwar kungiya mai suna IFESOWAPO Youth Traders Mile 12 International market dake cikin garin Legas.
Taron kaddamarwar wanda ya samu halartar shugaban nin kungiyar da lyaye da ‘yan kasuwar mazauna sassa daban-daban dake cikin garin Legas, makada da mawaka da sauran al’umma baki daya.
Manyan baki a wajen taron sun hada da daya daga cikin Iyayen kasuwar ta mile I2, Alhaji Mamuda da wadansu wakilai na tsofaffin shugabannin kasuwar doya da ta ‘yan gwari da sarkin Hausawan Mile I2 Alhaji Haruna Jibirin, da sauran maka mantansu baki daya. Da yake gudanar da jawabin sa a wurin taron kaddamarwar, shugaban kungiyar ya cigaba da fadin dalilan da suka sanya suka kirkriro wannan kungiyar kuma suka kaddamar da ita a karkashin jagorancin Alhaji Sagir, dalilin da suka kafa kungiyar ta hadin kawunan matasan ‘yan kasuwar domin cigaba da tallafa wa kungiyarsu ta jin dadin matasan ‘yan kasuwa na wannan unguwa ta mile12 a game da harkokin kasuwancinsu da na rayuwar su baki daya.
Bugu da kari ya ce sabuwar kungiyar za ta cigaba da taimakawa gaya wajan wayar da ka matasa bisa ga bin hanyoyi zaman lafiya da sauran al’amurran da suka shafi harkokin rayuwarsu. Shi ma da yake nasa tsokacin a wurin taron, sabon shugaban kungiyar ta hadin kan matasan ‘yan kasuwa, Alhaji Sagir bayan ya kammala nuna farin cikinsa na samun shugabancin kungiyar, ya ce zai yi iyaka kokarinsa wajen tafiyar da harkokin kungiyar da kuma samo hanyoyin ci gabanta baki daya.
Babban sakataren kungiyar, Alhaji Auwalu na Allah Kiru wanda shi ne ya gabatar da manya manyan baki a wurin taron, cewar ya yi babu shakka wannan kungiya tasu tana taka rawar gani kwarai da gaske a wajan matasan ‘yan kasuwa na cikin garin Legas inda ya ce tallafa wa matasan ‘yan kasuwar ne wajan harkokin kasuwancin su na yau da kullum, san nan kuma suna tallafa wa matasan musamman wadanda suka samu matsalar karayar arziki, in dai abu bai shafi sata ba za su sanya hannu ko baki ko aljihu su tabbatar da cewar sun fitar da dan kasuwar daga cikin wannan kangi.
Shi ma a nasa jawabin, Sarkin Hausawan Mile 12, Alhaji Haruna Jibirin, wanda ya yi wa mambobin kungiyar fatan alheri tare da basu shawarwari na hada kawunansu da kuma zaman lafiya a tsakaninsu bakidaya. Sauran jawaban da suka fito daga bakunan sauran al’umma a taron Alhaji Mamuda ne ya gabatar daya daga cikin iyayen kasuwar da sauran jama’ar da suka tofa albarkacin bakinsu. Dukkan jawaban sun ya karkata ne a wurin mambobin kungiyar na cigaba da zaman lafiya tare da hada kan junansu a jihar.